Daga Sayyadi Abubakar Sadeeq
Shahararren mawakin jam’iyyar APC Kuma mawakin Gwamnatin Shugaban kasa Muhammad Buhari Wato Dauda Kahuta Rarara ya jagoranci rukunin mawakan Kungiyar 13*13 Inda suka yi Waka Kan matsala tsaron data addabi kasar nan.
Kadaura24 ta rawaito a Cikin Wakar da Mai Magana da yawun Dauda kahuta Rarara Rabi’u Garba Gaya ya wallafa a Shafin na Facebook yace Kungiyar 13 13 ce ta yi wakar wadda take Magana a Kan matsala tsaron Nigeria.
A Cikin Wakar dai mawakan sun nuna gazawar Gwamnatin tarayyya wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta Musamman ta fuskar kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Kasar nan.
Mawakan sun tunawa gwamnatin irin nauyin dake kanta na inganta harkokin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a Nigeria.
” Kasata ita ce gaba, Ni banga kamarta ba, gwamnati ki fito ki Kara himma sha’anin tsaro,sai da tsaro arzikin Kasa ke dada cigaba”. Amshin Wakar kenan
Mawakan sun ja hankalin gwamnatin sosai da sosai, kan ta kara himma Sakamakon Mawuyacin halin da al’ummar Nigeria suka shiga a birni da karkara na rashin tsaro.
Ga Wani baiti daga cikin baitocin Wakar
” Yanzu fa Jama’ar Kasa kadan ke Muku uzirin, dan ko abun ya yawaita Kauye da cikin gari, ana Jin wai-wai ada yanzuga shi a zahiri, fatana a Yau ni da Kai mu dorata a mambari.” Baitin Rarara
Kadaura24 ta rawaito wasu daga cikin mawakan sun hadar da shi Rarara din da Nura m Inuwa da Aminu ala da Ali Isa jita da dai Sauransu.
Al’umma da dama dai sun yi mamakin Jin Wannan wakar daga Bakin Musamman Rarara, kasancewar yayi kaurin Suna wajen Kare gwamnatin tarayya da manufofin ta.