Daga Kamal Yakubu Ali
An bukaci Al’ummar musulmi da su kara kaimi wajen tallafawa Marayu da kayan sallah da kuma kula da ilimi da tarbiyyarsu.
Kadaura24 ta rawaito Shugaban Gidauniyar jundullah foundation Dr Adam Kamaluddeen Adam na ma’aji, shi ne ya bayyana hakan yayin da yake mika tallafin kayan Sallah da kudin Dinki ga Marayu 105 dake unguwannin Marmara , sheshe , Alfindiki, Sudawa da kuma Daneji .
Dr Adam Kamaluddeen ya bayyana cewar sun dauki gabarar tallafawa marayun ne domin koyi da fadin Annabi (S A W) na cewar a jikan Maraya, Wanda hakan zai kara masa hakuri. Ya kuma jaddada aniyar gidauniyar ta jundullah wajan ganin ta tallafawa marayu dake karamar hukumar Birni Musamman a wannan wata na Ramadan
Yace tallafawa marayu da kula da tarbiyyarsu abune da Allah yake farin ciki dashi, Adon haka ya bukaci Al’umma dasu zage damtse wajan aiwatar wadannan ayyuka da zasu Kai bayi Zuwa aljanna.
Shugaban Gidauniyar ta jundullah ya bukaci Gwamnati da masu hannu da shuni dake cikin al’umma, da su kafa wata cibiya mai karfi wacce zata dinga kula da rayuwar marayu, tare da daukar nauyin Karatun su.
wakilinmmu kamal ya kuma Ali ya bamu rawaito mana cewa Kungiyar ta gudanarda rabon tallafln a masallaci marigayi kamal Adamu Dake Unguwar marmara a Karamar Hukumar Birni da kewaye..