Daga Abubakar Sa’eed Sulaiman
Tsohuwar jarumar kannywood Farida Jalal ta bayyana cewa yanzu haka tana gudanar da yabon Annabi (S A W) a wuraren taron biki ko Suna ko maulidi da dai Sauransu.
Kadaura24 ta rawaito Farida Jalal ta bayyana hakan ta Cikin Shirin daga bakin Mai ita na BBC Hausa Wanda aka saka a Wannan makon .
Tsohuwar jarumar tace ba ita take rubuta kasidun ba, rubuta mata ake yi, sannan tace tana yin mamin din wakokoin Wasu Masu yabon musamman Waɗanda suka shahara.
” Ina hawa nayi mamin din wakokoin Zainab Ambato da Kuma na sayyada Nusaiba, Amma Nima Ina rerawa sannann na hau kayan na”. Inji Farida Jalal
Farida Jalal ta Kara da cewa ta yi kasidu ba Masu yawa ba, Kuma Yanzu haka tana Shirin Kara yin wasu, ko da aka tambayeta abun dake sata ba bacin rai, sai ta ka da baki ta ce “Yabon Annabi S A W”.
Kadaura24 ta rawaito Farida Jalal tsohuwar jaruma ce a kannywood wacce tauraronta ya haska sosai har ta dauki Lambar yabo a Shekara ta 2003.