Hukumar Fansho ta Kano ta ziyarci Sabon Shugaban Ma’aikata Usman Bala

Date:

Daga Sayyadi Abubakar Sadeeq

 

Hukumar fansho ta Jihar Kano ta sha Alwashin ba da cikakken hadin kai da goyon baya ga sabon shugaban ma’aikatan jihar nan Alhaji Usman Bala Gwagwarwa.

Kadaura24 ta rawaito Shugaban Hukumar ta fansho Alhaji Sani Dawaki Gabasawa ne ya bayyana hakan yayin wata Ziyarar girmamawa da taya murna ga Sabon Shugaban Ma’aikatan a Ofishin sa.

Alha Sani Dawaki Gabasawa Wanda Hon. Mai fada Bello ya Wakilta yace Hukumar fanshon ta ji dadi sosai da nadin da Gwamna Ganduje ya yiwa Alhaji Usman Bala Gwagwarwa.

Yace Suna fatan sabon Shugaban Ma’aikatan Zai Kara zage dantse wajen Kara inganta aiyukan Hukumar musamman ta fuskar tabbatar da Cewa kowacce Ma’aikata ta na biyan Hukumar abun da doka t bukaci a basu domin samun damar sauke nauyin da aka dora musu.

Kowa ya Sami Gwamna Ganduje yayi fice wajen biyan hakkokin yan fansho musamman kudaden su na wata-wata, Kuma yana Bakin kokarin sa wajen biyan kudaden garatuti na Ma’aikatan da suka kammala aiki”. Inji Dawaki Gabasawa

Da yake nasa jawabin Sabon Shugaban Ma’aikatan Jihar kano Alhaji Usman Bala Gwagwarwa ya godewa Shugabanni da Ma’aikatan Hukumar Saboda zuwan da sukai kafa da kafa don su taya shi murna.

Yace Hukumar fansho tana Cikin Hukumomin da yake fatan fara ziyarta domin duba hanyoyi da za’a bi don Magance Matsalolin da ake fuskanta a Hukumar.

“Ina sane da yawan alkaluman Mutanen da suka kammala aiki ba tare da an basu hakkokin su ba, Inda ya ce Kamar yadda Gwamna Ganduje yake kokarin sauke nauyin shi ma zai dafawa yunkurin gwamnan don warware Matsalolin Hukumar”. Inji Usman Bala

Usman Bala yayi fatan Shugabanni da Ma’aikatan Hukumar zasu bada hadin Kai domin samun nasarar da ake data.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...