Daga Kamal Yakubu Ali
Tsohon mashawarci ga Gwamnan jihar kano akan harkokin yada labarai Salihu Tanko Yakasai ya ce ya fice jam’iyyar APC Saboda Rashin sauke alkawuran da ta yiwa al’ummar Kasar nan.
Kadaura24 ta rawaito Salihu Tanko Yakasai ya bayyana hakan ne yayin taron Manema labarai a nan kano.
Salihu Tanko Wanda ake yiwa lakabi da Dawisu yace Jam’iyyar APC ta gaza sauke mafi yawa daga cikin nauye-nauyen data daukarwa yan Nigeria, dama abubun da ya kamata ace gwamnati ta yiwa al’ummar ta.
“Da ni Kai tallan jam’iyyar APC a dukkanin mafi yawa daga cikin jihohin Nigeria , Kuma mun yiwa al’ummar kasar nan alkawura Amma ni da kaina na gamsu da Cewa jam’iyyar ta gaza dauke alkawuran data yiwa yan kasa”. Inji Salihu Tanko Yakasai
Salihu Yakasai Wanda Gwamnatin kano ta dauke daga mukaminsa Saboda irin kalaman da yake yiwa Gwamnatin tarayya na fadin Rashin tabukawa Yan Kasa komai yace ya Dade yana fadawa gwamnatoci gaskiya tun lokaci da PDP ta ke Kan mulki.
“Saboda irin Matsalolin da Yan Ƙasar nan suke cikin na Rashin tsaro, rashin baiwa yan kasa kyakykyawar rayuwa ,Sanya Yan kasa cikin Mawuyacin halin dama Wasu Matsalolin hakan tasa na fice daga jam’iyyar APC a wannan rana”.inji Salihu Yakasai
Tanko Yakasai yace nan gaba kadan Zai baiyana Inda Zai Koma domin cigaba da gwagwarmayar Siyasa.