Daga Rukayya Abdullahi Maida
Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji, (wazirin Gaya) ya sanar da cewa zai tsaya takarar neman kujerar takar gwamana a jihar Kano a Jam’iyyar APC 2023.
Kadaura24 ta rawaito Alhaji Usman Alhaji ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da Gidan Talabijin na Rahama dake nan Kano .
Sakataren gwamnatin yace Yana da abubu masu tarin yawa da ya ke gudanar wa Idan ya zama gwaman jihar Kano kamar yadda Gwamna Ganduje ya yi.
“Shekaru 6 ana damawa dani a gwamnatin kano,dan haka ni na fi da cewa na gaji kujerar gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje a zaben 2023″ inji Usman Alhaji
Alhaji Usaman Alhaji yace Idan Allah ya bashi dama zai Dora ne akan duk Aiyukan alkhairi da gwamnatin Ganduje ta gudanar domin ciyar da Jihar gaba.
” Ganduje ya faro aiyukan alkhairi Masu tarin yawa Kuma duk dani aka faro su don hakan Zan Dora a duk Inda ya tsaya ,haka akai a Jihar Lagos har Jihar ta kai Matakin da take yanzu , haka ma farfesa zulum ya yi a jihar Borno, to nima idan na Sami dama haka zan yi”.inji Usman Alhaji
Yanzu dai shi ma Sakataren Gwamnatin ya shiga sahu su Murtala Sule Garo da Kabiru Alhassan Rurum da A A zaura wajen neman takarar kujerar gwamnan jihar kano a shekara ta 2023