Daga Abubakar Sa’eed Sulaiman
Ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ‘yan wasan kwaikwayo ke ƙoƙarin cimma shi ne tabbatar da cewa masu kallo ba su manta da fuskokinsu ba dangane da wasu ayyukan da sukai Waɗanda za a Rika so a kwaikwayesu.
Don haka ne ma wasu Jaruman wasan kwaikwayo suka zana sunayensu da fuskokinsu a zukatan da yawa daga cikin masoyansu ta yadda ko da suka suka bar sana’ar, har yanzu magoya bayansu na tunawa da su, kuma suna sha’awar ganin sun dawo harkar.
Kadaura24 ta yi karin haske kan wasu ‘yan wasan baya da ‘yan Najeriya za su so su sake Ganin fuskokinsu a akwatunan Talabijin dinsu Saboda da irin rawar da suka taka a baya.
Sadiya Gyale
Sadiya Muhammed wacce aka fi sani da Sadiya Gyale ta kasance daya daga cikin fitattun fina-finan Kannywood da ta taba yi. A tsakanin shekarar 2004 zuwa 2010, jarumar ta kasance ba ta cikin harkar shirya fina-finai ne kawai Saboda ta yi aure.
Sadiya Gyale ta kasance shahararriya a masana’antar fim saboda yadda ta iya taka duk rawar da aka ba ta yadda ya kamata. Hakan ya sanya ta zama tauraruwa a masana’antar fim a matsayin daya daga cikin fitattun jarumai da suka ja zarensu sosai a kannywood. Jarumar dai ta shafe shekaru da yawa ba ta fitowa a Fina-finan kannywood, Kuma yan kallo na mararinta sosai tun bayan da ta bar masana’antar a Shekara ta 2010.
Sadiya Gyale ta fito a fina-finai kamar, ‘Yar Film, Albashi (The Salary), Armala, Bakar Ashana (Burned Out Match), Balaraba, Dan Yola, Duniyar mu, Gidan Gado, Gidan Iko, Gudun Kaddara, Gwamnati, Gwanaye, Jamhuriyya, Jaraba, Kauna, Kishiya ko Yar Uwa, Kishiya ko Yar Uwa 2, Makuwa, Rintsin Kauna, Surkulle, Taurari, Tutar so da Ummi da sauransu.
Fati Muhammad
Fati Muhammed ta kasance shahararriya a Kannywood, a yayin daurin aurenta da Sani Mai Iska, ta samu damar jawo dimbin jama’a zuwa wurin bikin.
Jarumar ta kuma shahara a lokacin da ita da mijinta suka tafi Ingila zuwa wani aikin duk da dai aurenta bai dade ba ya mutu kuma ta dawo Najeriya.
Da zuwanta jarumar tayi kokarin komawa harkar fim amma bata yi nasara ba. Daga baya ta auri da kanin Ali Jita, kuma auren bai yi karko ba.
Abu na karshe da aka ji a labarin jarumar shi ne lokacin da ta shiga siyasa, a zaben 2019 inda jarumar dai ta kasance kodinetan yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar.
Ita ma dai ta ja zarenta sosai da sosai Inda tayi farin jini a wajen masu Shirya Fina-finai da daraktoci da Masu kallo.
Ta fito a Fina-finan kannywood kamar su Sangaya, Mujadala, sarkagiya da dai Sauransu.
Ibrahim Maishinku
Jarumi Ibrahim Maishinku ya kwashe shekaru da dama yana shiga fastocin Fina-finai Saboda irin rawar da ya Rika takawa a masana’antar fina-finan Kannywood. A wancan zamani, da wuya kaga fim din Hausa kaga ba jarumi Ibrahim maishunku ba ne Jarumin fim din. Ya dade yana haskawa a Kannywood kuma ya lashe kyaututtuka da dama na kansa da kuma fina-finan da ya fito a ciki.
An daina ganin fuskar jarumin a Fina-fina saboda wasu dalilai da ba a san su ba, hasken tauraronsa ya fara raguwa a hankali. Ko da yake wasu ’yan fim sun yi kokarin dawo kan bakarsa, amma yunkurinsu ya ci tura. Jarumin ya kuma gwada sa’arsa a siyasa, amma bai iya yin wani tasiri ba.
Sai dai Kadaura24 ta tattaro cewa wasu masu shirya fina-finai na kokarin sake farfado da tauraron jarumin ta hanyar shirya masa shirin talabijin Mai dogon zango da suke shirin yin nan ba da jimawa ba.
Tahir Fagge
Tahir Mahammad Fagge ya kasance daya daga cikin jagororin masana’antar fina-finan Hausa. Jarumin ya bar masana’antar tsawon shekaru kafin ya dawo. Tarihi ya nuna cewa Tahir Fagge yana daya daga cikin ’yan fim din da suka yi harkar Fina-fina kuma ya dawo ya cigaba da taka rawa ba tare da wata matsala ba.
Bayan dawowarsa masana’antar, jarumin ya cigaba da harkar kuma rahotanni na baya-bayan nan sun nuna cewa jarumin ya koma Abuja inda a halin yanzu yake jagorantar wani Gidan gala.