Buhari ya magantu Kan rikicin Shugabanci a APC

Date:

 

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi gargaɗi ga shugabanni da ƴan jam’iyar APC da su dena nuna wa juna yatsa da sa-in-sa a junansu, yayin da jam’iyar ke tunkarar babban taron ta na ƙasa a ranar 26 ga watan Maris.

Kadaura24 ta rawaito APC ta sake nutsa wa cikin rikici bayan da gwamnoni 19, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasir El-Rufai su ka hamɓarar da kujerar shugaban kwamitin riƙo na jam’iyar, Gwamna Mai Mala Buni, inda a ke zargin da umarnin shugaban ƙasa su ka aikata hakan.

Daga bisani sai Buhari ya ja kunnen ƴan jam’iyar da su ci gaba da jajirce wa da haɗa kai domin jam’iyar ta ci gaba da tafiya a kan gwadabenta na nasara da ta ke kai.

Buhari ya kuma buga misali da jam’iyar adawa ta PDP, inda ya ce duk karfin ta a ƙasar nan amma yanzu ta yi ƙasa.

A sanarwar da kakakin sa Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce APC ta kwashe kusan shekaru 8 tana mamaye sauran jam’iyyu sabo da ta buɗe kofar ta ga duk wanda yanke so ya shigo da ga wata jam’iya, babba ko karama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...