Daga Abdulrasheed B Imam
A kokarin sa na cigaba da ingantawa da samar da Sana’o’i ga matasa da maza Mata Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai natarayyar Rt Hon Alhassan Ado Doguwa sardaunan Rano ya sake sayen wasu gonaki domin fadada kamfanin sarrafa shinkafa dake yankin karamar hukumar Tudun wada.
Cikin Wata sanarwa da Mataimaki na musamman ga Shugaban Majalisar wakilai Auwal Ali Sufi ya aikowa Kadaura24 yace Hon Alhassan Ado Doguwa ya biya kudi kimanin Naira miliyan biyu da dubu dari takwas domin bunkasa Wannan masana’anta, wadda itace ta farko a tarhin yankin.
Rahotanni sun nuna babu wani Dan majalisar Tarayya da yayi irin Wannan aikin na kafa kamfanin sarrafa shinkafa a duk fadi jihar kano in ba Sardaunan Rano ba
Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai tar Rt Hon Alhassan Ado Doguwa yayi nazari wajen kawo Wannan aikin Alheri domin kakkabe Zaman kashe wando a tsakanin matasa dake yankin kano ta kudu baki Daya dama bunkasa harkokin noma a yankin.
Tuni Dai aka biya kudi kimanin Naira miliyan biyu da dubu dari 8 ga masu gonakin da suka amince suka sayar, domin aiki Zai ciyar da al’ummar Kananan Hukumomin Doguwa da Tudun Wada cigaba.