Daga Umar Hussain Mai Hula
Hukumar Karbar Korafe-Korafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar kano ta sami korafe-korafe daga al’umma bisa yadda wasu gidajen Mai a jihar su ke amfani da wannan yanayi da ake ciki wajen sayar da mai sama da farashin da gwamnati ta kayyade na N165 da kuma wasu masu boyewa domin samun kazamar riba.
Daga korafe-korafen da Hukuma ta ci karo dasu akwai gidajen da ke sayar da Mai har sama da Naira Dari Biyu (N200) wanda wannan ya sabawa doka da kuma tsawwalawa al’ummar jihar kano.
Dangane da hakanne Hukuma ke jawo hankalin masu gidajen mai da su tabbatar da sun dawo bisa kan ka’ida ta sayar da man akan farashin gwamnati na Naira Dari da Sittin da Biyar (N165) akan kowacce lita.
Sanarwa da Jami’in yada labaran Hukumar Yusuf Abubakar, ya Sanyawa hannu Kuma ya aikowa Kadaura24 yace Shugaban Hukumar Barr. Mahmoud Balarabe ya ta ci alwashin daukar dukkan matakan da doka ta amince da su wajen ganin an hukunta masu karya dokar kasa da kuma tsawwalawa al’umma.
Sanarwar tace Hukumar zata cigaba da zagayawa gidajen sayar da Mai don tabbatar da ganin gidajen Man suna bin doka.
Daga karshe kuma Hukuma na kira ga al’umma da su sanar da ita duk gidan man da suka gani yana sayarwa al’umma Mai sama da farashin gwamnati da kuma masu boyewa.