Daga Rukayya Abdullahi Maida
A cigaba da shari’ar da ake gudanarwa tsakanin gwamnatin kano da kuma malamin makarantar nan Abdulmalik Tanko da sauran mutane 2 da ake zarginsu da kisan daliba Haneepha Abubakar a yau babbar kotun jiha mai lamba 5 dake Audu Bako ta sake zama domin cigaba da sauraron shari’ar.
kotun ta sanya wannan rana ne domin fara sauaron shaidu daga bangaran lawyoyin gwamnati, kuma tun da misalin karfe 10 na safiyar yau ne kotun ta zauna sai dai an bukaci ‘yan jaridu dasu fice daga zaman kotun kasancewar 2 daga cikin jami’an DSS ne zasu gabatar da sheda agaban kotun a don hakane aka bukaci yan jaridar dasu fita na tsawon mintina 30 wanda har sai da takai ga ma’aikatan jaridar sun kwashe tsawon sa’o’i 4 a wajen kotun.
kammala bada shaidar jami’an DSS guda 2 ke da wuya kotun taje hutun mituna 30 bugawar agogo karfe 2n rana ne aka bukaci manema labarai dasu dawo kotun a cigaba da sauraron shaida na gaba, inda babban lawyan gwamnati ya sake gabatar da shaida na 3 mai suna Inspector Ubale Usman daga sashin yaki da masu garkuwa da mutane na rundunar yan sandan jihar nan, wanda kuma a cikin shedun da aka bayar har da shaidu ababen nuni da suka hadar da vedio-vedio da shebur din da aka hako mamaciyar har ma da ragowar kudin da suka karba a hannun iyayen Hanifa da dai sauran su.
Bayan kammala Jin shaidar Dan sandan ne kotun ta sanya gobe alhamis domin cigaba da shari’ar.