Rasha ta ce ta kwace babbar tashar nukiliya ta kasar Ukraine

Date:

Gwamnatin Rasha ta gaya wa hukumar da ke sa ido kan harkokin nukiliya ta duniya cewa, a yanzu haka yankin da babbar tashar nukiliya ta Ukraine take, kusa da birnin Zaporizhzhia na kudanci yana karkashin ikonta.

Hukumar nukiliyar, IAEA, ta ce Rashawan sun ba ta tabbacin cewa ma’aikatan Ukraine da ke aiki a tashar na ci gaba da gudanar da ayyukansu.

Sai dai hukumar nukiliyar Ukraine ta ce tana tattaunawa da dukkanin tashoshinta na nukiliyar, kuma aiki na ci gaba da gudana a dukkanninsu.

Amma Darakta Janar na hukumar nukiliyar ta duniya, Rafael Grossi, ya shaida wa taron manema labarai cewa halin da ake ciki na da tayar da hankali

Ya ce abu mafi muhimmanci a nan shi ne, idan ana rikici, lalle akwai fargabarkai hari, ko kuma ma a samu hadarin tashin makaman.

Tashar Zaporizhzhia tana dauke da shida daga cikin na’urorin nukiliya 15 na Ukraine.

BBC Hausa ta rawaito kafin yanzu dai hukumomin da ke kula da nukiliyar Ukraine sun bukaci taimakon hukumar nukiliya ta duniya, da ta taimaka ta tabbatar da tsaro a cibiyarta ta Chernobyl da ke arewacin Ukraine, wadda dakarun Rasha suka kwace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...