NDLEA za ta hada kai da kungiyar kare hakkin dan Adam ta International Human Right wajen yaki da shaye-shaye a kano

Date:

Daga Aliyu Sufyan Alhassan

 

Iyaye da masu ruwa da tsaki na da rawar takawa wajen kawo karshen ta’ammali da miyagun kwayoyi a Kano.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugabar kungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta duniya reshen jihar kano wato International Human Right Movement Ambasada Zuhra Abdulhamid Hassan lokacin da ƙungiyar ta kai ziyara ofishin hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi wato NDLEA anan Kano.

Ambasada Zuhra tace ziyarar da suka kai hukumar tana da alaƙa da haɗa kai don yaƙar shan miyagun kwayoyi tsakanin matasa.

Makasudin ziyarar ta mu ita ce domin mu sami hadin kai da Hukumar NDLEA ,sannan mu Hada karfi da karfe don mu yaki matsala shaye-shaye sata fyade da su ka addabi al’ummar kasar nan.” Inji Amb. Zahra

Tace Hukumar ta yi alkawarin zata baiwa Kungiyar hadin kai da goyon baya domin su cimma abun da Kungiyar su ta International Human Right ta Sanya a gaban.

A nasa jawabin babban kwamanda hukumar NDLEA na jihar kano Abubakar Idris Ahmad ya sha alawashin hada kai da kungiyar domin tabbatar da magance shaye shaye a tsakanin matasa.

Ziyara tana da matukar muhimmanci Kuma mun tattauna da dama Waɗanda Suka jibanci cigaban jihar kano da Kasa baki daya.”inji Amb. Zahra

Yace akwai alaka tsakinin hukumar NDLEA da Kungiyar Saboda Hukumar su saboda Kungiyar tana Kare hakkin al’umma ne mu Kuma muna yaki da Masu Sha da fataucin miyagun kwayoyi, yace nan bada jimawa ba al’umma zasu ga alfanun hadakar mu da Kungiyar.

Daga bisa ya nada shugabar kungiyar kare haƙƙin ɗan adam hajiya Zuhra Abdulhamid Hassan a matsayin jakadiyar yaƙi da wannan dabi’a ta shaye shaye da ta’ammali da miyagun kwayoyi bisa sahalewar shugaban hukumar na ƙasa Gen Buba Marwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...