A wani jawabi da ya yi wa al’ummar kasar Rasha ta talabijin, shugaba Vladimir Putin ya yaba tare da godiya ga sojojin Rasha da ya yi iƙirarin cewa suna gudanar da ayyukansu a Ukraine yadda ya kamata.
Ya ce an ɗora wa sojojin nauyin aikin bayar da taimako ga jamhuriyar jama’ar Donbas – yankuna biyu da Rasha ta amince da su a matsayin masu cin gashin kai.
Kamfanin dillancin labaran Interfax ya ce Mista Putin ya kuma yi magana da shugaban Azarbaijan game da abin da ya bayyana a matsayin farmakin soji na musamman na Rasha.