KSADP ya kashe sama da Naira Miliyan Dari don farfado da bayen shanu a kano

Date:

Daga Sayyadi Abubakar Sadeeq
 A ranar Asabar din da ta gabata ne Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya kaddamar da cibiyar kiwon dabbobi ta Kadawa, wanda Shirin kula da noma da kiwo na jihar Kano, KSADP ya gyara tare da samar da kayan aiki, a kan kudi sama da Naira miliyan 103.
 Cikin Wata sanarwa da Jami’in yada labaran shirin Ameen K Yassar ya aikowa Kadaura24 ya ce har ila yau, aikin ya sake cika cibiyar da bijiman shanu guda biyar Waɗanda darajarsu ta Kai sama da Naira miliyan 9, da niyyar bayen shanu akalla 25,000 a shekara.
 A cikin shanun da za a yiwa bayen, ana tattara maniyyin bijimai shanun don a yi amfani da su don mata su samibciki domin su haifi ‘ya’ya masu dabi’un da ake so, kamar yawan nono da jurewar cututtuka.
 A yayin bikin wanda ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki a harkar kiwo da suka hada da kungiyoyin makiyaya, Gwamna Ganduje ya bayyana cewa, “wannan na daga burin ganin an inganta shanun mu na gida, ta yadda za a inganta kudaden shigar makiyayan mu da Kuma rage ya kalubalen da suke fuskanta”.
 Gwamnan ya ce gwamnatinsa na inganta harkokin bayen shanu a matsayin wani bangare na yunƙurin canzawa kiwo irin na gargajiya Zuwa kiwo irin na zamani don inganta harkokin tattalin arziki, kamar yadda ake yi a duniya.
 “Muna matukar godiya ga Bankin Raya Musulunci da Asusun inganta Rayuwa na LLF, ba wai don Kawai Gudunmawar da suke bayarwa a sha’anin noma da kiwo ba, har ma da sauran ayyuka da dama a fadin jihar, inda suka zuba jari a cikin su, da nufin magance kalubalen talauci, samar da wadataccen abinci da rashin aikin yi da ya addabi mutanen mu”, in ji shi.
 Babban jami’in kula da dabbobi na Ma’aikatar noma ta kasa , Dakta Olaniyan Alabi, wanda Dr. Gana ya wakilta, ya yabawa gwamnatin Ganduje bisa jajircewa da kuma kaunar da take yi wa sashen kiwon dabbobi, inda ya ce hakan ya yi daidai da kokarin gwamnatin tarayya na kawo sauyi a fannin domin bunkasa shi.
 Babban jami’in Shirin bunkasa noma da kiwo na Jiha, KSADP, Malam Ibrahim Garba Muhammad, ya ce aikin nasa wanda Bankin Raya Musulunci da Asusun inganta Rayuwar al’umma suke daukar nauyinsa, ya farfado da cibiyar bayen shanu a wani bangare na habbaka harkokin noma da kiwo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...

Idan mu ka rungumi Addu’o’i ba abun da Amurka za ta iya yiwa Nigeria – SKY

Shahararren ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas ya Magantu Kan Zargin raba Ramat da Kujerarsa

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas,...

Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar...