Wasu ɗaliban Najeriya ƴan asalin jihar Sokoto da rikicin Rasha ya rutsa da su a Ukraine sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta kwashe su domin suna ganin damar barin ƙasar zai gagara nan ba da dadewa ba idan lamarin ya tsananta.
Ɗaliban da aka bayyana guda 22 sun yi wannan kiran ne a zantawar da gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya haɗa ta kafar zoom da su tare da kuma iyayensu daga gidan gwamnatin jihar.
Sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar ta ce ɗaya daga cikin ɗaliban mai suna Aisha Kabir ta shaida wa gwamnan cewa halin da ake ciki a Kharkiv ya tsananta.
Rahotanni a safiyar Lahadi sun ce sojojin Rasha sun kutsa Kharkiv kuma ana gwabza faɗa a birnin na biyu mafi girma a Rasha.
“Muna jin ƙarar harbe-harbe, ko da yake ana ƙoƙarin tafiya da mu cikin bus zuwa Romania, amma direbobin suna jin tsoron za a iya kai masu hari, muna ganin jirgin ƙasa ne ba ya hatsari wanda za mu yi sauƙin ficewa.” In ji ɗalibar kamar yadda sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Muhammad Bello ya fitar ta bayyana.
Wani ɗalibin kuma Shuaibu Muhammad, ya ce suna fuskantar ƙalubale a Krakow, Poland domin ba isasshen abinci da wurin bacci mai kyau. “Daga Lviv zuwa Krakow tafiyar awa 12 ce, kuma yawancinmu ba mu san kowa ba da za mu yi magana da shi lokacin da muka iso.
Wasu sun ce suna fuskantar ƙalubale na yanayin sanyi da rashin tufafin da ya dace da bargon bacci.
Wata ɗaliba Zarah Ibrahimn ta bayyana fargabar cewa “ta ji ana faɗi daga gobe za a hana wa ƴan ƙasashen waje fita Lviv, tana mai jaddada cewa Kharkiv na tattare da hatsari”
A nasa ɓangaren gwamnan jihar ya yi wa ɗaliban alƙawalin cewa da su da sauran ɗalibai ƴan Najeriya za su fice daga Ukraine nan ba da dadewa ba kuma su dawo gida lafiya.
Gwamnan ya ce ya ba ma’aikatar kuɗi ta jihar umarnin ta tura wa ɗaliban da ke cikin mawuyacin hali tallafin kudi kimanin dala 200 zuwa 300.
Iyayen ɗaliban sun yaba kan yadda gwamnatin Sokoto ta nuna damuwarta da kuma tausayin ƴaƴansu tare da jan hankalin ƴaƴansu da su yi taka-tsan-tsan a yayin ficewa Ukraine.