Daga sabo Jigirya
Masarautar Kano ta baiwa kamfanin jirgin Air Peace wa’adin sa’o’i 72 da ya ba da Hakuri kan rashin girmamawar da sukai wa Mai Martaba Sarki Kano Aminu Ado-Bayero.
Kadaura24 ta rawaito Babban hadimin Sarkin, Isah Bayero, ne ya bada wa’adin lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Asabar din nan.
Isa Bayero ya bayyana cewa dole ne kamfanin jirgin ya karbi alhakin jinkirta tashin jirgin da Sarkin ya hawo daga Banjul wanda ya kai ga Rashin girmamawar da basu yi wa sarkin ba.
“Ina ba da wa’adin sa’o’i 72 ga Air Peace da su baiwa sarki hakuri, na farko dai sai sun bashi a hukuri a Manyan jaridun kasar nan, na biyu Kuma su bashi hakuri su day sarkin, in Kuma ba Haka ba zamu bi kadin abun da sukai”.
Ya kuma yi watsi da ikirarin da kamfanin jirgin ya yi na bai wa sarkin damar sauya Masa jirgi zuwa Wanda zai je Abuja.
“Ni da kaina na nemi kamfanin Air Peace na ba wa sarkin damar shiga jirgin su zuwa Abuja; Daga nan za mu taho zuwa Kano amma suka ce shi ma jirgin da Zai tafi abujan ya cika,” in ji Isa Bayero.
Isa pilot yace jinkirin da suka samu daga Banjul, shi ne ya yi sanadin isowarsu Legas a Makare, Kuma Kamfanin na Air Peace shi yake da alhakkin kula da su Amma ba su Yi hakan ba Kuma Suka barsu hakan nan.”
“Abun da Kamfanin na Air Peace suka yi abu ne na rashin kwarewa kuma za mu yi iya kacin kokarinmu don daukar matakan da suka dace akan rashin da’ar da akai sarkin mu.” Inji Isa Pilot
“Wannan cin mutuncin ba Sarki kadai aka yiwa ba, a’a ga mutanen Kano baki daya Kuma ba zamu zura Ido hakan ta cigaba da faruba ba”.