Hukumar zaɓe a Najeriya INEC ta sanar da jadawalin babban zaɓe na 2023, inda za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa ranar Asabar 25 ga watan Fabarairun 2023.
Shugaban INEC Farfesa Mahmud Yakubu ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Asabar.
Kazalika, za a gudanar da zaɓen ‘yan majalisun tarayya tare da na shugaban ƙasar.
BBC Hausa ta rawaito Zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi zai gudana ranar 11 ga watan Maris na 2023 ɗin.
A cewarsa, an zaɓi ranar ce saboda a tabbatar an yi aiki da sabuwar dokar zaɓe, wadda ta tanadi cewa wajibi ne a bayyana ranar zaɓen aƙalla kwana 260 kafin kaɗa ƙuri’a.
Ya ƙara da cewa hukumar za ta wallafa sauran tanade-tanaden dokar zaɓen “a lokacin da ya dace”.
Sauran ranakun da suka shafi babban zaɓen:
- 28 ga Fabarairu 2022: Wallafa ranakun gudanar da zaɓe
- 4 ga Afrilu zuwa 3 ga Yunin 2022: Gudanar da zaɓen fitar da gwani na jam’iyyu da kammala sauraron ƙorafe-ƙorafe
- 10 zuwa 17 ga Yunin 2022: Aika sunayen ‘yan takarar shugaban ƙasa da ‘yan majalisar tarayya ga INEC ta shafinta na intanet
- 1 zuwa 15 ga Yulin 2022: Aika sunayen ‘yan takarar gwamna da ‘yan majalisar jiha ga INEC ta shafinta na intanet
- 28 ga Satumban 2022: Fara yawon kamfe na ‘yan takarar shugaban ƙasa da ‘yan majalisun tarayya
- 12 ga Oktoban 2022: Fara kamfe na ‘yan takarar gwamna da ‘yan majalisar jiha
- 23 ga Fabarairun 2023: Kammala kamfe na ‘yan takarar shugaban ƙasa da ‘yan majalisar tarayya
- 9 ga Maris na 2023: Kammala kamfe na ‘yan takarar gwamna da ‘yan majalisar jiha