Daga Sayyadi Abubakar Gwagwarwa
Tshon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa yana nan daram a jam’iyyarsa ta PDP .
Kwankwaso ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala taron da ya jagoranta a Abuja na Kungiyar cigaban Najeriya mai suna The National Movement yayin wata zantawa da Premier Radio dake kano.
Sanata Kwankwaso ya ce sun Kafa Sabuwar Kungiyar ne domin nemawa kasar nan mafita Sakamakon Mawuyacin halin da take ciki.
” An dade ana Cewa Zan bar jam’iyyar PDP Kuma ko a jiyama sai da Wasu Kafafen yada labarai Suka Rika Cewa Yau Zan fice daga PDP domin Kafa Sabuwar jam’iyyar, to Ina sanar da Jama’a cewa Ina nan daram a PDP”. Inji Kwankwaso
Tsohon Gwamnan na kano yace Sabuwar Kungiyar ta TNM tana da mambobi daga ko’ina a Cikin jam’iyyun APC da PDP da Sauran jam’iyyu dama Waɗanda basu da jam’iyya, kuma yace bayan Kaddamar da Kungiyar zasu cigaba da yada manufofin Kungiyar a jihohi da Kananan Hukumominsu.