Ina nan daram dam a PDP – Kwankwaso

Date:

Daga Sayyadi Abubakar Gwagwarwa

Tshon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso  ya bayyana cewa yana nan daram a jam’iyyarsa ta PDP .

Kwankwaso ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala taron da ya jagoranta a Abuja na Kungiyar cigaban Najeriya mai suna The National Movement yayin wata zantawa da Premier Radio dake kano.

Sanata Kwankwaso ya ce sun Kafa Sabuwar Kungiyar ne domin nemawa kasar nan mafita Sakamakon Mawuyacin halin da take ciki.

An dade ana Cewa Zan bar jam’iyyar PDP Kuma ko a jiyama sai da Wasu Kafafen yada labarai Suka Rika Cewa Yau Zan fice daga PDP domin Kafa Sabuwar jam’iyyar, to Ina sanar da Jama’a cewa Ina nan daram a PDP”. Inji Kwankwaso

Tsohon Gwamnan na kano yace Sabuwar Kungiyar ta TNM  tana da mambobi daga ko’ina a Cikin jam’iyyun APC da PDP da Sauran jam’iyyu dama Waɗanda basu da jam’iyya, kuma yace bayan Kaddamar da Kungiyar zasu cigaba da yada manufofin Kungiyar a jihohi da Kananan Hukumominsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...

Idan mu ka rungumi Addu’o’i ba abun da Amurka za ta iya yiwa Nigeria – SKY

Shahararren ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas ya Magantu Kan Zargin raba Ramat da Kujerarsa

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas,...

Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar...