Daga Ibrahim Aminu Riminkebe.
Kimanin majinyata su 1171 ne suka amfana da aiki da kuma bada tallafin magunguna kyauta ga marasa lafiyar da suka ci gajiyar aikin wanda Kungiyar yan kasuwa yan asalin karamar hukumar Kabo dake jihar kano wato Kabo Zone Traders Association da kuma hadin gwaiwa Ƙungiyar likiticin musulmai ta kasa reshen jihar Kano suka gabatar da aikin har na tsahon kwanakin biyu wanda gudana a babban asibitin karamar hukumar ta Kabo.
Daga cikin aikin da aka yiwa marasa lafiyar sun hadar da yin tiyatar Ƙoda, cire tsakuwa, aikin idanu, saka hakora, bada magunguna, da dai makamantan su duk a Asibitin na kabo.
Kadaura24 ta rawaito cewar guda daga cikin masu ruwa da tsakin na Ƙungiyar yan kasuwar yan asalin karamar hukumar ta Kabo wato Alhaji Mamuda Liman Zangon Kabo, ya nuna farin cikin sa Saboda yadda aikin ya kasance, yana mai bayyana cewar wannan bashi ne karon farko da Kungiyar ta yan kasuwar suke gudanar da irin wannan aikin.
Alhaji Mamuda Liman Zangon ya Kara da cewar babban abun jin dadi shi ne baya ga karamar hukumar Kabo akwai marasa lafiyar da suka zo daga kananan hukumomin Ungogo da kuma Gezawa domin cin gajiyar aikin kyauta.
Alhaji Mamuda Zangon Kabo yace babban abunda ya Kara karfafa musu gwaiwa wajan gudanar da aikin shi ne yadda a halin yanzu mutane manya da yara suka fama da larurori iri daban daban, amma kuma basu da kudin da zasu je asibitin dan duba lafiyar tasu.
Kazalika Alhaji Mamuda Liman Zangon Kabo ya mika godiyarsa ta musamman ma a madadin dukkanin shuwagabannin Ƙungiyar yan kasuwar yan asalin karamar hukumar ta Kabo dama saura masu ruwa da tsaki na cikin Ƙungiyar bisa irin namijin kokarin da Kungiyar likitici musulmai ta kasa reshen jihar Kano mazan su da matan su dama sauran jami’in lafiya sukai bisa yadda suka yi tsayiwa irin ta daka wajan ganin sun yi marasa lafiyar aikin abunda yake damun su dama yadda suke nuna kauna ga al’ummar karamar hukumar ta Kabo.
Wasu daga wadanda suka ci gajiyar aikin dama bada magunguna kyauta da Kungiyar yan kasuwa yan asalin karamar hukumar Kabo hadin gwaiwa da Kungiyar likitici musulmai suka gabatar a babban asibitin karamar hukumar ta Kabo sun nuna matukar farin ciki dakuma jindadin yadda babu zato babu tsammni ka kawo musu daukin abunda yake damun su tsahon shekara da shekara tare yin kira ga yan kasuwar dama likiticin daka su gajiya wajan gudanar da wannan aikin alkhairi.