NUT ta yabawa Ganduje bisa nadin sabon jami’in kula da Tsangaya a Jihar Kano

Date:

Halima M Abubakar
Kungiyar malamai ta Najeriya reshen karamar hukumar Gwale ta bayyana nadin Malam Mustapha Adamu sabon jami’in  kula da Tsangaya na Jihar kano a matsayin wanda ya dace.
 A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren kungiyar reshen karamar hukumar Kwamared Auwalu Shuaibu Ja’e kuma aka aikowa Kadaura24.
Sanarwar ta kuma bayyana Malam Mustapha Adamu a matsayin jami’i mai kwazo da sadaukar da kai wajen bunkasa ilimi a kananan hukumomi da jiha baki daya.  .
Sanarwar ta ce kungiyar ta yabawa gwamnatin jihar bisa wannan nadin da kuma kokarin da take yi na inganta fannin ilimi a jihar kano.
 Malam Mustapha Adamu har zuwa lokacin da aka nada shi, shi ne Shugaban sashin Larabci a Hukumar Ilimi ta Karamar Hukumar Gwale.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

NAHCON ta sanar da ranar da za a fara jigilar Maniyatan Nigeria zuwa kasar Saudiyya

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Hukumar kula da aikin hajji ta...

Hisbah ta rushe wajen da aka ce sawun Ma’aiki ya fito a jihar Kano

    Hukumar Hisbah ta kai samame tare da rushe wani...

ƴan siyasa ne su ka kashe Arewacin Nigeria — Inji Gwamna Uba Sani

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa ‘yan...

Shugaban Karamar hukumar Bagwai ya kaddamar da aikn gada ta sama da Naira Miliyan 160

Daga Shu'aibu Sani Bagwai   Karamar hukumar Bagwai a jihar Kano...