Bayan Hukuncin kotu, Ganduje ya yi zazzafan Maratani ga yan G7

Date:

Daga Kamal Yakubu Ali

 

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya mayar da zazzafan martani ga tsagin su Malam Ibrahim Shekarau biyo bayan hukuncin da Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke akan rushe hukuncin da wata kotu a Abuja tayi na rushe Shugabancin APC a matakin mazaɓu da ƙananan hukumomi ɓangaren Ganduje.

Kadaura24 ta rawaito cewa bayan hukuncin da kotu ta yanke a safiyar wannan rana, gwamna Ganduje yace Banza 7 sun faɗi wan-war akan rashin bin ka’idojin jam’iyya da kuma amincewa da jagorancin sa.

Yan banza 7 abun da sukai Kamar Suka dusa ne da damuna ko kuma ginin da aka yi fandushonsa da toka Kuma ace za a dora Masa ginin bulo”inji Ganduje

Ganduje Wanda yayi Magana Cikin Wani faifen video da yake Jawabi ga Wasu Yan Majalisu da Sauran mukarraban Gwamnatin Jihar Kano ya godewa Shugaban Rika na Jam’iyyar APC Mai Mala Buni bisa kokarin Ganin ya sulhun su day yan G7.

Ganduje ya Kuma yabawa dukkanin yan Jam’iyyar APC na Kano da matasa maza da Mata bisa goyon bayan da Suke baiwa Gwamnati da APC a Jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu ta ɗaure wani ɗan Tiktok mai wanka a tsakiyar titunan Kano

    Wata kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya...

Damuna: Mun shirya inganta wuraren tsayarwar motocinmu – Kungiyoyin Direbobin na Kano

Kungiyar matuka motocin kurkura ta jihar Kano da Kungiyar...

Rasuwar Aminu Ɗantata babban rashi ne ba ga Nigeria kadai ba – Mustapha Bakwana

Daga Zakaria Adam Jigirya   Tsohon Mai baiwa gwamnan Kano shawarawa...

Gwamnatin Kano ta yabawa Tinubu saboda gyarawa da bude NCC DIGITAL PARK

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnatin jihar Kano ta yabawa Gwamnatin...