Gwamnatin Kano ta musanta zargin Kwashe Kayan Aikin Cibiyar killace Mutane ta ‘yargaya

Date:

Daga Khadija Abdullahi
 Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta yi fatali da zarge-zargen da ake yi akan cibiyar killace mutanen da Suka Kamu da cututtuka Masu yaduwa ta ‘Yargaya a matsayin maras tushe balle makama.
 Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai daga sashin hulda da jama’a na hukumar kula da Manyan asibitocin bisa umarnin ma’aikatar lafiya ta jihar tare da bayyanawa Kafafen yada labarai a matsayin su na musanta zargin da akan yi cibiyar dake ‘Yargaya.
 Sanarwar ta ce labarin da Wasu Kafafen yada labarai na yanar gizo suka rawaito cewa an rufe cibiyar killacewar, kuma an kwashe kayan aiki dake ciki tare da kashe mai gadin, Inda Sanarwar tace labarin ba gaskiya ba ne bashi da tushe ballantana makama.
 Tun a kanun labaran aka yi kuskure Inda aka cewa “an rufe cibiyar killace mutanen Masu Covid-19”, bayan Kuma a Hukumance ba a kiran Cibiyar da suna ‘Yargaya Covid-19 Centre ba, a maimakon haka ‘Cibiyar killace mutane ta Yargaya ce saboda an kafa ta tun kafin bayyanar cutar Covid -19.
 “Don fayyace komai gwamnatin jihar Kano ce ta kafa cibiyar ta ‘yargaya a lokacin annobar zazzabin Lassa domin a kebe mutanen da suka kamu da cutar a yi musu magani a wurin domin kada su yada cutar Sauran Mutanei ,” in ji sanarwar.
 Dangane da zargin an kwashe kayan aikin, sanarwan ya musanta Zargin Inda ta bayyana cewa kamfanin Mudassir da Brothers Textile ne ya gyara Cibiyar a shekarar 2020 a karo na biyu na Covid-19 don tallafawa gwamnatin jihar Kano a yakin da take yi da cutar, kuma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje, inda ya tabbatar wa mutanen jihar cewa babu abin da ya lalace a Cikin cibiyar.
 A Sanarwar da Jami’in hulda da Jama’a na Hukumar kula Asibitoci ta jiha Ibrahim Abdullahi ya aikowa Kadaura24 yace a Wannan labarin ba a yi wa ma’aikatar lafiya ta jihar Kano adalci game da labarin ba, Kuma mun fahimci an yi hakan ne da gangan Saboda a badawa Ma’aikatar Suna da Kuma haifar da hargitsi da tashin hankali a jihar kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...