Wasu da ake zargin’yan fashi ne sun kashe wata mata a gidan ta da ke unguwar kadawa a jihar kano.
Waɗanda suka kashe matar matar mai suna Rukayya sun ji wa ƴaƴanta biyu rauni.
Abin ɗaure kai game da yadda aka kashe ta shi ne babu wanda ya san takamaimai lokacin da lamarin ya faru, sai dai ana kyautata zaton sun shiga gidan ne bayan magariba a ranar Asabar.
Duk da cewar mazauna unguwar sun ki yarda BBC ta naɗi muryoyinsu, amma sun bayyana cewa akwai magina a jikin gidan da shagunan sayar da kayayyaki haka kuma a iya saninsu ba su ga shigar wani baƙo gidan ba haka kuma ba su ga fitar waɗanda suka gudanar da wannan aika-aika ba.
Sai bayan da mai gidanta ya dawo ne sannan aka san halin da ake ciki. Ana zargin da taɓarya suka daketa a kai har wuri biyu, sannan suka daki ɗanta a kansa sau ɗaya. Sai ƙurjewa da aka samu a fuskar wadda take shayarwa.
Mijin marigayiyar ya gaza yin magana saboda halin da yake ciki.
Yanzu haka babu kowa a gidan marigayiyar kuma ana zaman makoki a gidan iyayen marigayiyar da ke Unguwar Madatai a cikin birnin Kano.
Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin kuma ta ce tana gudanar da bincike.
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce an kama mutum biyar da ake zargi da hannu a lamarin.
Ko a watan da ya gabata sai da aka kama wasu da ake zargi da kashe wata yarinya ƴar shekara biyar mai suna Hanifa.