Cikar Faizu Alfindiki Shekara 1 a mulki, Yan Municipal Riba Suka kirga ko faduwa ?

Date:

A yau ne shugaban karamar hukumar birni da kewaye, Kwamared Faizu Alfindiki, ya cika shekara daya a Mulki, mun tattara wasu aikace-aikacen cigaban da shugaban ya samar cikin shekara daya.
Kadaura24 ta rawaito Gabanin Samun nasarar kowanne Shugaba akwai bukatar ya tsara manufar da yake son cimma ba Wai ya hau mulki ba tare da ya tanadi abubuwan da ya kamata yayiwa al’ummar ba.
Kwararrun shugabanni masu hangen nesa ne, suke da kyakkyawar manufa dangane da inda suka dosa da abin da suke ƙoƙarin cimmawa.
Gwamnatin Municipal karkashin jagorancin Hon. Faizu Alfindiki ya samu nasarori da dama ta fuskar shimfida manyan ayyuka a karamar hukumar birni da kewaye, inda ta samu ci gaba sosai duk da kalubalen tattalin arzikin da kasar nan ke fuskanta sakamakon annobar cutar covid-19 guda 19 da ta addabi duniya.
Kamar yadda ta yi alkawari, Gwamnatin Comrade Faizu Alfindiki ta himmatu wajen Ginawa da Ƙirƙirar manufofi, Ayyuka da shirye-shiryen Inganta Lafiya da Ilimi.
1-) Comrade Faizu Alfindiki, a farkon shigarsa ofis ya kafa Kwamitin Ilimi wanda Professor Muhammad Ibrahim Daneji ke jagoranta domin sanya idanu tare da binciko matsalar data addabi harkar koyarwa a karamar hukumar, a kokarin shugaban na bunkasa harkar ilimi tare gyara harkar Ilimin tun daga tushe.
2-) Shugaban Karamar Hukumar Kano Comrade Faizu Alfindiki a ranar Laraba 3 ga Watan Nuwamba, ya fara bayar da tallafin kayayyakin ilimi na miliyoyin Nairori ga Makarantun gwamnati da makarantun islamiyya na karamar hukumar.
Kayan sun hadar da:
Computer Books (2,000), Record of Work (2,000), Kira ga Matasa Books (77), White Uniform (7,770 Yrds), Blue Uniform (2,740 Yrds), Exercise 20L (4,00 Bks), Chalks (290), School Log Book (15), Normal Register (302), Daily Attendance (39), Admission Register (58), Visitors Book (34), Movement Book (34), Duster (161Nos), Black Board Ruler (92), World Globe (19pcs), Globe Chart (71pcs), Exercise Book 40L (348Bks), Biro (6pkts), Pencil (14pkts), Colour Pencil (294pkts), Izal (6Gallon), Lesson Plan (69), Brooms (104Nos), School Cert (13), Plastic Ruler (465), Wood Ruler (69), C/A (9,300), Record and Diary (93).
3-) Comrade Faizu Alfindiki, A ranar 9 ga Nuwamba, 2021 ya kafa kwamiti don tantance dalibai ‘yan asalin karamar hukumar birni domin cin gajiyar tallafin karatu wato Scholarship, kimanin mutane (1832) ‘yan asalin KMC aka tantance su.
4-) Comrade Faizu Alfindiki, a yanzu haka yana gina katafariyar makarantar Primary Islamiya a Mazabar Sharada, Kuma aikin anci kaso 90% nan gaba kadan za’a kammala.
5-) Comrade Faizu Alfindiki, ya raba kayan abinci na kusan N500Million
An raba kayan abinci zuwa cibiyoyi 16 da ke fadin karamar hukumar.
Kayan da aka damkawa ko wacce cibiya sun hada da:
-Buhun-hunan shinkafa 8
-Wake Buhu 2
-Gero Buhu 3
-Fulawa Buhu 2
-Suga Buhu 3
-Makarono Katon 5
-Man Ja Jarka 5
-Man Gyada Jarka 2
-Dabino Buhu 1
-Takeaway 2000
-Abun Wanke Hannu Katan 1
-Takunkumi Katan 5
6-) Comrade Faizu Alfindiki, ya gyara makarantar firamare ta Aminu Kano Islamiya da ke Unguwar Zaitawa
7-) Comrade Faizu Alfindiki, ya rabiyawa mutane 400 da suka fadi Qualifying kudin zana jarabawar NECO kyauta
😎 Comrade Faizu, ya bayarda tallafin kudi naira ₦750,000 domin kara tallafawa harkokin ilimi ga kungiyar dalibai ta Sharada.
9-) Comrade Faizu Alfindiki yayi rabon magunguna kyauta ga asibitocin karamar hukumar Kano Municipal, asibitocin da aka bayar sun kasance kamar haka;
– Chedi PHC
– Sharada PHC
– Tukuntawa MPHC
– Gandu PHC
– Yan awaki PHC
– Ali Musa PHC
– Emir Place HC
– Datti Wudilawa HC
– D/ Anadi HC
– Daneji HC
– Madatai PHC
– Alfindiki HC
– Unguwar Gini PHC
– Mayanka PHC
– Zubairiyya HC
– Fuskar Gabas PHC
10-) Comrade Faizu Alfindiki, ya samarwa mutane 10 da ke da sha’awar AIR FORCE da LAND ARMY aiki.
11-) Comrade Faizu Alfindiki ya dauki Matasa 354 aiki (Temporary) akan tattara kudaden shiga,
12-) Zagayan gani da ido ga Makarantun da ke karkashin kulawar Karamar hukuma
13-) Comrade Faizu Alfindiki, ya yi Empowerment na Dubu Goma-Goma ga mutane 801 Maza da Mata
15-) Comrade Faizu Alfindiki, ya gina bandakuna a fadin Kasuwar kurmi, domin magance matsalar fitsari a bakin kwata kuma wanda ke sanadiyar ganin tsiraici
16-) Comrade Faizu Alfindiki, A ranar 24 ga watan nuwamba 2021, Shugaban Karamar hukumar ya gwangwaje ‘yan Vigilante Group da Mota Kirar Ford Galaxy, ‘Yan Sanda, Civil Defence Corps da kuma DSS duk sun rabauta da sabbin mashina kirar Hero (Hunter) guda goma (10) domin kara inganta tsaro a fadin karamar hukumar da kewayen ta.
17-) Biyan kudin mai (Petroleum) naira dubu Dari-Dari a duk karshen wata ga dukkanin Division din da ake dasu a fadin karamar hukumar KMC.
18-) Comrade Faizu Alfindiki, ya bayarda gudunmawar ₦200,000 ga makarantar Islamiyya dake kofar mata, Hashik School of Arabic and Islamic Studies.
19-) Municipal KAL-KAL sabon shiri ne wanda shugaban karamar hukumar ya kafa wanda ke zagayawa Unguwanni domin zakulo kananun matsaloli kamar, gyaran kwalbati, sanya Interlock da kuma futulun wuta.
20-) Comrade Faizu Alfindiki nya tallafa wa ma’aikata 10  na kungiyar NULGE, biyar daga ciki sun samu  ₦500,000 yayin da sauran suka samu ₦1,000,000
21-) ComradeFaizu Alfindiki, ya kammala biyan kudaden rage radadi ga iyalan tsofaffin ma’aikata 10 da suka rasu shekaru uku da suka gabata, ₦260,000
22-) Comrade Faizu Alfindiki, Ya gyara bututun ruwa daga Mandawari zuwa Kwanar Goda
23-) Comrade Faizu Alfindiki, ya kafa kofofi 20 masu karfi don kewaye, Marmara, Akwa, Alfindiki, Kududdufawa, Mazan Kwarai da Kwanar Goda a kokarin magance matsalar tsaro a yankin KMC, gami da wani yanki a karamar hukumar Gwale.
24-) Comrade Faizu Alfindiki, ya dauki nauyin mutane 300 don yi musu aikin ido kyauta
25-) Daukar nauyin sanyawa mutane 100 hakora kyauta.
26-) Comrade Faizu Alfindiki, ya raba buhunhunan shinkafa da kudin cefane ga gidajen malaman musulunci sama da 100 da kuma limaman masallatan juma’a, domin bikin murnar Maulidin Annabi (S.A.W)  a ranar 5 ga October 2021.
27-) Comrade Faizu Alfindiki Ya Bada Gudummawar ₦500,000, Domin Gyaran Kujerun Dalibai Tare Da Gyara Ajujuwan karatu a makarantar Abubakar Sadik Junior Secondary Secondary school.
28-) Faizu Alfindiki, ya ba da gudummawar ₦500,000 a cikin Madarasatu Tahfizil Kur’an Wa Ulumiddin Daneji.
29-) Comrade Faizu Alfindiki, ya ba da gudummawar dubu ₦500,000 a yayin bikin yaye daliban makarantar Sheikh Adamu K. Namaaji.
30-) Comrade Faizu Alfindiki, ya bada tallafin kudi ₦200,000 ga Subulussalam Islamiyya Littahafizul Qur’an Kabara
31-) Comrade Faizu Alfindiki ya bayarda ₦500,000 ga Makarantar “Madarasatul Jilani Li Tahfizuk Qur’an Alfindiki”
32-) Comrade Faizu Alfindiki, ya bayarda gudunmawar ₦200,000 ga makarantar Islamiyya dake kofar mata, Hashik School of Arabic and Islamic Studies.
33-) Comrade Faizu Alfindiki, ya baiwa ko wanne kansilan mazaba ₦500,000 domin gudanar da ayyuka.
34-) Comrade Faizu Alfindiki, ya baiwa Madarasatul Babba Danagundi Littarbiyatul Aulad Wattajwidil Qur’an Islamiya gudunmawar ₦250,000
35-) Comrade Faizu Alfindiki, ya gwangwaje Makarantar Mahe Islamiya dake Indabawa da kyautar Fili
36-) Comrade Faizu Alfindiki, ya baiwa Madarasatul Tanbihuddeenil Islam dake koki gudunmawar ₦200,000
37-) Comrade Faizu Alfindiki, a lokacin da ya kai ziyarar saukar karatun Alkur’ani Makarantar Nurussalati, ya ba wa dalibai 27 kyautar kudi Dubu Goma-Goma ga masu sauka, tare da atamfofi, shaddodi da kuma kudi ₦270,000
38-) Comrade Faizu Alfindiki, ya ba da gudummawa Fili ga makarantar ASASUL ISLAM PRIMARY SCHOOL don fadada makarantar.
Da Wannan ne al’ummar Karamar Hukumar Birni da kewaye suke sambarka bisa aiyukan Raya Kasa da cigaban al’umma da Faizu Alfindiki ya gudanar a Shekara guda, sai dai sun yi fatan Zai Kara zage damtse wajen ganin a Shekara ta biyi yayi Aiki fiye da Wanda yayi a bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...