‘Yan Majalisar Dokokin Zamfara 18 Cikin 22 sun amince da tsige mataimakin gwamnan jihar

Date:

Majalisar Dokokin Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ta jefa uria’r amincewa da tsige Mataimakin Gwamnan Mahdi Aliyu Gusau daga kan muƙaminsa da gagarumin rinjaye.

Yayin wani zama a jiya Alhamis, ‘yan majalisa 18 cikin 22 ne suka amince da ɗaukar matakin yayin da ɗaya tak ya ki amincewa.

Haka nan, ‘yan majalisar sun nemi Alƙalin Alƙalai na Zamfara Mai Shari’a Kulu Aliyu ya kafa kwamatin da zai binciki Mahdi bisa zargin saɓa sashe na 190 da 193 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

Dangantaka tsakanin mataimakin gwamnan da uban gidansa Gwamna Bello Muhammad Matawalle ta yi tsami tun lokacin ya gwamnan ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a bara amma Mahdi ya ci gaba da zama a PDP.

Honorabul Shamsudden Hassan Bosko, shi ne Shugaban Kwamitin yada Labarai na majalisar kuma ya shaida wa Haruna Shehu Tangaza yadda aka yi wannan zaman.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...