Daga Sayyadi Abubakar
Yan siyasa sun lalllasa ma’aikatan Gwamnati da ci daya mai ban haushi.
A Wani bangare na bikin cikar Shugaban Karamar hukumar Kumbotso Hon Hassan Garban kauye farawa murnar cika shekara guda a matsayin Shugaban Karamar hukuma Kumbotso an shirya wani wasan sada zumunta domin kyautata alakar aiki tsakanin ma’aikatan Gwamnati na Karamar hukumar da Masu mukaman Siyasa.
Wannan dai a kunshe Cikin wata Sanarwa Mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin yada labarai na wasan shazali farawa wadda kuma ya aikowa Kadaura24.
Wasan Wanda ya gudana a filin wasa na Kumbotso, Yan siyasa sun yiwa ma’aikatan Dakan sakwara bayan da aka tashi 1-0, inda Yan siyasa suka samu nasara bayan dawowa daga hutun Rabin lokaci ta hannun kamalu Tanda SA komai da Ruwan ka.
Bayan kammala wasan Shugaban Karamar hukumar Hon Hassan Garban farawa ya Mika Babban Kofi ga matainakinsa a matsayin jagoran Masu mukamai Kuma Captain wato Hon Shamshu Abdullahi Kademi, Yayin da su Kuma ma’aikata suka karbi karami ta Hannun CPO.
Tarihi ya nuna cewa ba’a taba samun wani lokaci da ma’aikatan Gwamnati da yan siyasa suka hadu domin yin wasan Sada Zumunci a karamar Hukumar Kumbotso ba, sai wannan lokaci.