Zamu Maida hankali wajen shuka Tazargade don magance cutar Maleria a Kano – Masu Kayan lambu

Date:

Daga Kamal Yakubu Ali

 

Kungiyar masu sana’ar kayan lambu ta kasa reshen jihar kano ta yabawa gwamnati bisa shiryawa ya’yan kungiyar bita domin Sanar da su sabbin dabaru na zamani don su inganta sana’ar su.

Kadaura24 ta rawaito Shugaban kungiyar malam Aliyu kabara shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a kano.

Yace gwamnatin jihar kano tare da hadin gwaiwar kamfanin Samar da magunguna na A.Z ne dauki nauyin gudanar da bitar domin wayar da kan masu sana’ar kayan lambu dabarun zamani domin bunkasa harkokinsu.

Malam Kabiru bayan bayyana godiyar da ga Waɗanda suka Shirya musu bitar, yace masu sana’ar zasu maida hanakali wajan Samar da irin Tazargaje a lambunansu domin yin amfani dashi wajan Samar da maganin zazzabin cizan sauro da ake fama dashi.

Yace zasu yi amfani da Sabbin dabarun da suka koya a bita domin tallafawa yan kungiyar wajan bunkasu harkokinsu.

Ya kuma kira ga yan kungiyar wadanda basuyi rejista da dasu ba da su je su yi domin su amfani da tsare-tsaren da suka bijiro dasu a Koda yaushe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...