Bunkasa Noma: Shirin KSADP na samun gagarumar nasara a Kano

Date:

Daga Aminu Indabawa

Gagarumin shirin nan na bunkasa noma da kiwo na Jihar Kano KSADP shirin da gwamnatin Jihar Kano karkashin Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya samu tallafin kudi daga bankin addinin musulunci dake Jidda da wasu hukumomi wanda hukumar bunkasa aikin gona ta KNARDA ta ware wani bangare domin lura da shirin don bunkasa shi.

A daidai lokacin da shirin ya shiga shekara ta biyu cibiyar Sassakawa Africa Association (SAA) tayi taron masu ruwa da tsaki a shirin da suke hada da ICRASAT, IITA kamfanunonin saye da sayarwar kayan amfanin gona da bunkuna domin jin rahotannin irin abubuwan da suke gaba a shirin.
Taron ya samu halartar Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna wanda shine shugaban kwamitin, Wanda Gawuna ya samu wakilcin babban sakatare a ma’aikatar gona ta Jihar Alhaji Balarabe Karaye ya Wakilta ya nuna jin dadi da gamsuwar sa akan yadda shirin yake gudana.
 Shugaban Sassakawa na kasa Prof. Sani Miko ya yi tsokaci akan yadda cibiyar tasa ta himmatu wajen ganin ta sauke nauyin da ake dora mata.
 Shi ma shugaban hukumar KNARDA Dr. Junaidu Yakubu Muhammad da shugaban gudanar da shirin na jiha Mal. Ibrahim Garba sun yaba da yadda suka tabbatar da gaskiya da Sassakawa keyi wajen aiwatar da shirin na KSADP.
Mahalarta taro musamman masu ruwa da tsaki sun tattauna inda a qarshe aka gamsu anyi nasara kuma za’a ribanya nasarar anan gaba.
 Daga bisani aka raba babura guda (29) ga malaman gonar da ake wannan aiki dasu qari akan guda (90) da aka raba a shekarar data gabata, inda shugaban shirin na Jiha Mal. Ibrahim Garba yayi albishirin sahalewar cibiyar ta Sassakawa siyen guda (100) nan gaba duba da irin kokarin da sukayi na siyan ingatattun babura.
Suma wadanda suka rabauta da wadannan babura sun nuna jin dadin su, tare da aniyar rubanya kokarinsu wajen gudanar da ayyukan dake gabansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya bijiro da harajin da zai sa farashin man fetur ya karu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙaddamar...

Sabbin Nau’o’in cutar Shan Inna 4 sun bulla a Kano

Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar...

NDLEA ‘Yan Sanda da Gwamnatin Kebbi Sun Karyata Jita-jitar Samar da Filin Jirgin Sama na Boye a jihar

  Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta...

Kotu a Kano ta kawo karshen Shari’ar wata Tunkiya

Daga Dantala Uba Nuhu, Kura An kawo ƙarshen shari’ar wata...