Aisha Buhari ta ziyarci Kano don yin ta’aziyyar Hanifa Abubakar

Date:

Daga Maryam adamu Mustapha
Uwar gidan Shugaban Kasa Aisha Buhari ta ja hankalin gwamnatin Kano da ta dauki matakan kariya ga Kananan Yara don gudun kara afkuwar abin da ya faru da yarinyar nan Haneefa Abubakar da malaminta ya yiwa kisan gilla a nan Kano.
Uwar gidan shugaban kasa ta bayyana hakan ne lokacin da ta zo Gidan Gwamnatin Jihar Kano don yiwa Gwamnati da  Iyayen Hanifa Abubakar ta’aziyyar  Rasuwarsu .
Aisha Buhari ta yabawa Gwamnatin Jihar Kano bisa matakan data dauka tun faruwar lamarin, Sannan  ta ce saurin yanke hukunci ga Waɗanda aka Samu da Wannan laifi zai kwantar da hankalin iyaye musamman mata.
Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya jaddadawa al’ummar Kano cewa gwamnatin Kano ba za ta kara ko minti guda ba wajen sanya hannu, Idan Kotu ta yanke hukuncin kisa akan Waɗanda ake Zargi.
Uwar gidan Shugaban Kasar ta Ziyarci Fadar Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero domin yi Masa ta’aziyyar rashe-rashen da akai a Kano a yan watannin baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya bijiro da harajin da zai sa farashin man fetur ya karu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙaddamar...

Sabbin Nau’o’in cutar Shan Inna 4 sun bulla a Kano

Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar...

NDLEA ‘Yan Sanda da Gwamnatin Kebbi Sun Karyata Jita-jitar Samar da Filin Jirgin Sama na Boye a jihar

  Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta...

Kotu a Kano ta kawo karshen Shari’ar wata Tunkiya

Daga Dantala Uba Nuhu, Kura An kawo ƙarshen shari’ar wata...