Daga Abdulrasheed B Imam
Bayan bayyana ficewarsa daga jam’iyya mai mulki ta APC a karshen shekarar da ta gabata ta 2021, shugaban majalisar malamai ta jihar Kano, Sheik Ibrahim Khalil, ya shiga jam’iyyar ADC, wanda kuma nan gaba kadan za’a shirya taron karbarsa cikin jam’iyyar.
Bayanin komawa jam’iyyar ADC da malamin yayi, na kunshe cikin wani sako da shugaban jam’iyyar na jihar Kano, Shu’aibu Ungoggo, ya gabatar ga manema labarai a yau juma’a.
Cikin bayanin nasa, Shu’aibu Ungoggo, yace malamin ya shigo jam’iyyar tasu ta ADC ne tare da Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa na jami’ar Bayero, da kuma wasu malaman jami’a guda takwas da suka rufa masa baya, a kokarinsu na ganin cewa an ceto jihar Kano daga halin da ta ke ciki, a cewarsa.