Daga Ussaini Minjibir
Wutar lantarki mai ƙarfi ta haddasa gobarar da tayi sanadiyyar mutuwar maigida da matarsa da ɗansu mai shakara uku a aduniya.
Kadaura24 ta rawaito gobarar ta tashi da misalin karfe goma sha biyu na daren alhamis din data gabata a unguwar Maƙera dake kadawa miltara, inda ta ƙone mata da miji da kuma ɗansu mai shakara uku a aduniya.
ƙanin maigidan mai suna Umar Yahaya ya shaidawa Kadaura24 cewa Marigayin mai suna Anwar Yahaya ƙaninsa ne mai kimanin shekaru talatin da biyu ita kuma matar mai suna Fatima Idiris tana ma ɗauke da juna biyu Allah ya karɓi rayuwar su.

Ya kuma ce gobarar ta tashi ne sakamakon wutar lantarki mai ƙarfi da aka kawo a unguwar tasu kuma yayi ƙoƙarin fitowa daga ɗakin amma ya al’amarin ya gagara.
Sai da safe ne makwabta suka haura suka tarar tuni rai yai halinsa.
An kuma yi musu sallah kamar yanda addini ya tanadar, Inda aka kai su maƙabartar unguwar miltara .
shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano comrade Sale Aliyu jili ya kai musu ziyarar ta’aziyya Inda lamarin ya afku, tare kuma da basu kayan tallafi da suka haɗa da katifu da kwanan rufi da shinkafa da masara da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum.