Tura Kananan Yara Bara Laifin waye ?

Date:

Daga Khadija Abdullahi

Matsalar tura kananan yara bara a manyan birane da sunan neman ilmin addini babban kaluable ne wanda ke janyo cece kuce a mabambamtan lokuta a Cikin al’umma.

Yanzu haka mataslar yawon kananan yara da suke yawo a manyan titunan manyan birane ya zama babbar matsala musamman a wannan lokaci da ake fama da matsalolin Rashin Tsaro.

 

Shi laifin wanene? Iyayen da ke turo ‘ya ‘yan nasu da cewar wai sun tura su neman ilmi , ba tare da hado su da abincin da zasu ci ba, Kayan da zasu saka, abubuwan bukatunsu na yau da kullum ?, ko kuwa malamam da ke karbarsu haka nan zikau ba abinci da sauran kudaden da zasu kula da yaran.

Time Express Nigeria ta rawaito shi dama hakkin Malami ne bayan ya baiwa yaro Ilimi Kuma ya kula da lafiyar da Sauran bukatunsu ?

Shin me ya kamata hukumomi su yi don magance wannan kalubale?

Gaskiya ya kamata gwamnatoci su cigaba da tsayawa tsayin daka wajen daukar matakan da suka dace domin shawo kan wannan matsalar.

Su kuma iyaye suji tsoron Allah su dauki nauyin da ke kansu wajen ciyar da yayan nasu da kuma daukar dawainiyarsu.

Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum suna ganin dole ne kowanne bangare su yi kokarin sauke nauyin da ya rataya a wuyansu, ta haka ne Kawai za a Magance Wannan matsalar.

Kadaura24 ta rawaito matsalar barace-baracen kananan yara a kowanne Lokaci a Kasar nan Kara tu’azzala yake yiwa Kuma hakan na taka muhimmiyar rawa Wajen Kara Zama barazana ga tarbiyya da Zaman Lafiyar al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...