Shekarau ya bayyana Sharuddan Sulhu da tsagin Ganduje

Date:

Nasiba Rabi’u Yusuf
Tsohon Gwamnan Jihar Kano Kuma Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce a shirye yake ya sasanta da bangaren Gwamna Ganduje.
 Shekarau ya bayyana cewa sulhun zai kasance ne a bisa sharuddan adalci da ga daukacin ‘ya’yan jam’iyyar APC a jihar Kano.
 Hakan na kunshe ne a cikin wani sakon murya da aka fitar a ranar Laraba inda ya bayyana abin da ya faru yayin wani taron sasantawa da shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC da gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, da sauran mambobin kungiyar suka gudanar a Kano.
 Malam Shekarau ya bayyana cewa kwamitin bai yanke hukunci kan kowane batu ba bayan tattaunawar amma sai dai ya yi kira ga bangarorin da su hada kai domin a samu zaman lafiya, inji kamar yadda dailynews24 ta rawaito.
 ”Mun shaida wa kwamitin cewa a shirye muke don tattaunawa kan zaman lafiya amma da sharudda.  Sharuɗɗan kuwa sune mutunta ƴan jam’iyya, daidaito da adalci a tsakanin kowa, domin a kare haƙƙin kowa.
 ‘’Gwagwarmayar da muke yi ba wai don kawo hargitsi ko rashin mutunta kowa ba ne, amma don tabbatar da cewa kokarin ya samar da daidaito ga kowa.
 Allah Madaukakin Sarki ya jaddada cewa sulhu alkhairi, amma ba bukace mu da mu kasance masu hankali da gaskiya da tabbatar da adalci wajen aiwatar da aikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...