Gwamnatin kano ta fara wayar da kan mutanen karkara don Samar da wutar Lantarki mai amfani da Hasken Rana

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida
Shugaban karamar hukumar Garko Alhaji Salisu Musa Sarina ya yabawa Gwamnatin jihar kano bisa aiyukan raya kasa da take aiwatarwa al’ummar jihar.
Kadaura24 ta rawaito Alhaji Salisu Sarina ya bayyana hakan ne yayin da kwamashinan Ma’aikatar raya karkara da cigaban al’umma na jihar Kano Alhaji Musa Iliyasu kwankwaso ya zayarci fadar hakimin yankin.
Shugaban karamar hukumar wanda daraktan Mulki na yankin Alhaji Halilu Kunya ya wakilta yace duba da tarin aiyukan da gwamnati mai ci yanzu ta ke gudanarwa a fadin jahar nan ya zama wajibi a yaba mata.
Da yake nasa jawabin kwamashinan Ma’aikatar raya karkara Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso yace sun ziyarci yankin ne don wayar da kan al’umma akan Shirin gwamnati na samar da hasken wuta mai amfani da hasken rana ga al’umma musamman mutanen karkara.
 Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso   wanda mai taimaka masa na musamman Alhaji Abdulhamid Yusuf ya wakilta yace shirin zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin al’ummar jihar nan, kuma shirin zai baiwa matasan yankin yadda ake gyaran kayayyakin na’ura mai amfani da hasken rana.
Anasa bangaren hakimin Garko Dandarman Gaya Alhaji Adamu Abdullahi Adamu wanda Alhaji Mamuda Abba ya wakilta ya godewa gwamnatin jiha bisa nuna damuwarta ga Jama’ar jihar nan a inda ya bayar da tabbacin goyan bayan da hadin kan iyayen kasa.
A wani cigaban kuma kwamashinan ya makamanciya ziyarar ga karamar hukumar Wudil mataimakin shugaban karamar hukumar Alhaji Labilu Ismail ya tarbeshi a cibiyar yada addinin yankin.
Alhaji Labilu Ismail ya bayyana aniyar karamar hukumar na marawa dukkan kyawawan tsare- tsaren gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje baya da ya kamata domin samun nasarar inganta rayuwar al’umma.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu matasan Kano biyu a Benue

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi...

Rashin Jami’ar Mallakin jihar a shiyyar Kano ta Arewa na kokarin bayar da yankin baya – Alh. Mustapha Ahmad Gwadabe

Daga Shehu Hussaini Ahmad Getso An bukaci Gwamnatin jihar Kano...

Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Almuharram a Nigeria

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji...

Yan uwan wata mata sun zargi Asibitin Malam Aminu Kano da sakaci wajen mutuwar yar uwarsu

Daga Sadiya Muhammad Sabo   Yan uwan wata mata da ta...