Matsalolin Nigeria sun sanya Aminu Dantata zub da hawayen takaici

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maids

 

Fitaccen attajirin nan dake kano Alhaji Aminu alhasan Dantata ya zubar da hawaye a wajen kaddamar da wani  littafin da dantatan ya dauki nauyin fassarawa a jami’ar Bayero ta kano

Kadaura24 ta rawaito Dattijon attajirin ya zubar da hawayen ne a Lokacin da yake gabatar da jawabinsa, inda ya ce  matsalolin kasar nan kullum kara karuwa suke kuma shugabannin kasar babu ruwansu da halin da yankasar suke ciki.

 

Yace abun takaici ne yadda ake kashe mutane kullum a kasar nan kuma shugabannin a kowanne mataki sun gaza daukar matakin da zai dakile matasalolin rashin tsaron.

 

Dantata ya kuma ce baya ga matsalar tsaro akwai matsaloli masu tarin yawa da suka yiwa talakawan kasar nan katutu, musamman matsalar tashin hauhawar kayan masarufi da sauran kiyan amfanin yau da kullum .

 

Ya bukaci shugabannin da su ji tsoron Allah su rika yin abun da zai saukakawa al’ummarsu, yace su sani Allah zai tsayar da su ranar kiyama ya tambayesu akan yadda suka bari ake kashe mutane babu gaira babu dalili.

“Yanzu bana tsoran kowa, kuma ba na tsoron komai akwai abin da nake so shi ne in mutu ina musulmi kuma in cika da kalmar shahada don na hadu da mahaliccina salun alun”. Inji Dantata

Dattijon arzukin ya ce mutane su ji tsoron Allah su gyara halayensu su sasanta da junansu duk wanda yasan ya ci hakkin dan uwansa ya yi kokari su sasanta tun kafin su je Lahira sannan ya kara fashewa da kuka saboda halin da yankin arewa ya samu kansa a ciki

Yana zubar da hawaye Alhaji Aminu Dantata ya ce Allah bazai gyara mana ba har sai mun gyara da kan mu kuma yana jawabin ne yana karanto ayoyin kur’ani kuma ya ce shi ba abin da bai gani ba a duniya domin shekarunsa 94

A jawabin mai alfarma sarkin musulmai Alhaji dr sa adu Abubakar na uku, ya yi wa al’ummar kano ta aziiyyar mutanen da su ka rasu a wannan Lokacin har ya roki Alhaji Aminu Dantata akan ya jagoranci tattara ilimin Dr Ahmad Bamba na BUK guri guda wanda ya gabatar a Lokacin Rayuwarsa

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...