Sabuwar hukumar hana bara a kano ta kama mabarata sama da 300

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Gwamnatin jihar kano ta ce ta kama almajirai sama da 300 maza da mata yara da manya a birnin kano.

Da yake zantawa da manema labarai Shugaban Hukumar hana barace-barace a jihar kano Malam Albakari Mika”il yace mafi yawan wadanda suka kama ba almajirai bane da suke zuwa makaranta ba.
Albakari yace gwamnati ba zata saurarawa duk Wanda ta kama sau biyu ba, zata mika su ga kotu domin ta yanke musu hukunci kamar yadda ya dake.
Yace za su mayar da wasu yaran gaban iyayensu wasu kuma musamman wadanda aka same su Suns shaye-shaye za a mika su ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi da kuma mika wasunsu ga rundunar yan Sanda.
Malam albukari ya kara jaddada cewa za su cigaba da kamen almajirai da masu gararanba a kwaryar birnin kano da kewaye domin tsaftace kano daga mabarata .
Wasu daga cikin almajiran da aka kama sun shaidawa kadaura24 cewa an kama su ne da misalin karfe 3 na dare a unguwannin Sabon gari, Tarauni titin IBB da dai sauransu .
Da yawansu sun ce sun yi nadama tare da bada tabbacin ba za su cigaba da gararanba a gari ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Yusuf ya taya Dangambo murnar zama shugaban kungiyar mawallafa labarai ta internet na Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Hajjin bana: Za mu yi duk abun da ya dace don kyautata walwalar alhazan Jihar Kebbi – Amirul Hajji

Daga Ibrahim Sidi Muhammad Jega.   Shugaban kwamitin aikin hajin bana...

Bayan dawo da Gwadabe Anti daba, Yansanda sun kama yan daba 33 a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar Yansanda ta Kasa reshen jihar...

Sabon Rikici ya Barke a Jam’iyyar NNPP ta Karamar Hukumar Dawakin Tofa

Rikici ya barke a cikin jam’iyyar NNPP ta karamar...