Wasu ‘Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da Mahaifiyar wani Dan Majalisa a Kano

Date:

Daga Maryam Muhd Zawaciki
Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da mahaifiyar Isiyaku Ali Danja, shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin jihar Kano da tsakar daren ranar Talatar data gabata.
 Majiyoyi sun ce maharan sun shiga gidan Hajiya Zainab da ke karamar hukumar Gezawa da misalin karfe 1:00 na dare dauke da makamai, inda suka tilasta mata fita daga dakinta suka kuma tafi da ita.
 Dan majalisar, Isyaku Ali Danja ya tabbatar da sace mahaifiyar tasa ga ‘yan jarida a ranar Laraba, yana mai  cewa har yanzu wadanda suka yi garkuwa da ita ba su tuntubesu  ba.
Jaridar Time Express ta rawaito Isiyaku Ali Danja, shi ne tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kano kuma wakilin Gezawa a majalisar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...