Matashi Mai Shekaru 21 ya hallaka yarinyar yar shekaru 13 bayan yayi Garkuwa da ita ta Gane shi a Kano

Date:

Dagan Maryam Muhda Zawaciki

Rundunar yan sanda ta  kasa reshen jihar kano tace ta kama wani matashi da ya yi garkuwa da wata yarinya yar kimanin shekaru 13 da haihuwa kuma ya kasheta saboda ya fahimci yarinyar ta gane shi.
Kadaura24 ta rawaito Jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP Abdullahi Haruna kiyawa ne ya bayyana hakan ta sahihin shafinsa na Facebook.
 Yace a ranar 21/06/2021 suka samu rahoto daga wani mazaunin garin Tofa da ke karamar hukumar Tofa a jihar Kano cewa an yi garkuwa da ‘yarsa mai suna Zuwaira mai shekaru 13 tare da bukatar ya bayar da kudin fansa har naira miliyan daya.  An nemi (N1,000,000.00) daga baya aka koma Naira Dubu Dari Hudu (N400,000.00).  Yayin da ake tattaunawa don neman kudin fansar, aka gano gawar yarinyar a wani kango inda aka yankata kuma aka binne a wajen.
 ” Bayan samun wannan mummunan rahoton, an ziyarci wurin, aka tono gawar, likitoci kuma suka tabbatar da mutuwarta, inda muka mika gawar ga ’yan uwanta don a yi mata jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada”. Inji kiyawa
 Sanarwa ta ce hakan tasa kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, fsi, ya umurci rundunar ‘Operation Puff Adder’ karkashin jagorancin SP Shehu Dahiru  wadanda Allah ya basu ikon kama Wanda ake zargi da aikata laifin mai suna Auwalu Abdulrashid, wanda ake kira da Lauje, Dan kimanin shekaru 21 a garin Tofa, karamar hukumar Tofa, jihar Kano a kauyen Dan marke, karamar hukumar Dambatta, jihar Kano a ranar 09/09/2019.  01/2022, watau kwanaki 202 bayan faruwar lamarin.
 DSP Kiyawa ya kara da cewa wanda ake zargin ya amsa cewa, shi kadai ne ya yi garkuwa da wadda ya kashe,sannan Wanda ake zargin ya ci gaba da cewa, a ranar 07/06/2021, ya yi garkuwa da wani kanin marigayiyar mai suna Muttaka, mai shekaru 3 a garin Tofa, karamar hukumar Tofa, jihar Kano, inda ya bukaci a biya shi kudin fansa naira miliyan biyu.  (N2,000,000.00), daga baya ya dawo Naira Dubu Dari (100,000.00) ya kuma bar yaron a makarantar Dawanau Special Primary School, Dawakin Tofa LGA, Jihar Kano.
 Sanarwar ta ce  za a gurfanar da Wanda ake zargin a gaban kotu domin a girbar abun da ya shuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...