Sama da yara miliyan 3 za a yi wa rigakafin cutar Polio a kano cikin watan Janairu – in ji Ganduje

Date:

Daga Halima Isa Jauro
 Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa sama da yara miliyan 3 da dubu dari 6 ne za a yi wa rigakafin cutar shan inna a gangamin  Makon Haihuwa da kula da lafiyar Yara na watan Janairu.
 A cewar sa,aikin gangamin za a gudanar da shi ne tare da jami’an kai daukin gaggawa yayin annoba, inda jami’an rigakafin za su bi gida gida don yi wa yara ‘yan kasa da shekaru 5 rigakafin cutar shan inna.
 “Manufar Makon Haihuwa da kula da Yara da Mata masu juna biyu shi ne inganta harkokin kiwon lafiya ga mata masu juna biyu da ‘ya’yansu.” Inji shi.
 Cikin sanarwar da Babban sakataren yada labaran Mataimakin gwamna Hassan Musa Fagge ya aikowa kadaura24 yace Gwamnan wanda mataimakinsa Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta ya bayyana hakan a ranar Lahadi a karamar hukumar Ungogo yayin kaddamar da gangamin makon haihuwa da kula da yara da mata masu juna biyu a jihar.
 Ya kara da cewa gwamnatin jihar Kano ta himmatu sosai wajen samar da isassun kayan aikin kiwon lafiya ga al’ummarta saboda haka… “bai kamata mu yi kasa a gwiwa ba wajen ganin mata masu juna biyu suna zuwa asibiti a fadin jihar”.
 Gwamnan ya yabawa Gwamnatin Tarayya, Shugabannin Kananan Hukumomi, Masarautu da kuma masu bada tallafi a fannin kula da lafiya bisa jajircewar da suka yi na ganin an samu ci gaba mai ma’an, don haka ya bukace su da su kara kaimi kan nasarar da aka samu a aikin.
 A nasa bangaren, kwamishinan lafiya na jihar Dr.Aminu Ibrahim Tsanyawa ya bukaci iyaye su bada hadin kai ga jami’an rigakafi domin ganin an samu nasarar aikin.
 Sauran masu ruwa da tsaki da suka yi jawabi a yayin bikin sun hada da wakilin Sarkin Kano, Dankadan Kano Dr. Bashir Muhammad, shugaban karamar hukumar Ungogo Alh.Abdullahi Garba Ramat da wakilan kungiyoyin bada tallafi.

1 COMMENT

  1. Usually I do not learn article on blogs, however I wish to say that
    this write-up very pressured me to try and do it! Your writing
    taste has been surprised me. Thank you, quite
    great article.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...