Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta Soke Jarrabawa saboda Yajin Aikin ‘Yan adaidaita Sahu

Date:

Daga Maryam Muhd Zawaciki

Jami’ar Yusuf Maitama Sule to soke jarrabawar da za ta gudanar da karfe 8 zuwa 11 na safe a gobe Litinin biyo bayan shirin tafiya yajin aiki da matuka babun adaidaita sahu suka yi.

Kadaura24 ta rawaito wanna na kunshe cikin wata sanarwar da shugaba kwamitin shirya jarrabawar Jami’ar Dr Yau Datti ya fitar ranar Lahadin nan.

Sanarwar ta ce kwamitin zai tuntubi shugaban Jami’ar domin yanke hukunci kan makomar sauran jarrabawar da za a rubuta.

Tun kwanaki uku da suka wuce yan Sahun suka raba takardun Kira ga matukan da su shiga yajin aikin mako guda don nuna adawarsu ga sabunta koriyar lamba da hukumar KAROTA ta ce suyi.

Haka kuma tun da yammacin yau Lahadi aka ga sun fara sanya ganye alamar yajin aikin na man daram babu gudu babu ja da baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...