Gwamnatin Taliban, a ƙasar Afghanistan ta sanar da wata sabuwar doka da ta shafi dukkan al’ummar kasar.
Dokar ta baiyana cewar, da ga yanzu duk wanda ya makara bai je masallacin Juma’a ba har a ka fara Huɗuba, to za a yi masa bulala 25.
Dokar ta ce hukuncin babu babba, babu yaro, in da gwamnatin ta ce “saboda haka hukumomin Gwamnatin Taliban su ke kira ga dukkan al’ummar ƙasar Afghanistan da su kiyaye wannan doka, wajen zuwa Masallacin Juma’a akan kari.”
Daily Nigerian ta rawaito Gwamnatin ta baiyana cewar dokar za ta fara ne daga gobe Juma’a, shi ya sa ma a ka shiga kasuwanni ana sanar da jama’a dokar a yau.
A gefe guda kuma, Gwamnatin ta samar da isassun bulalai ga dukkan jami’an tsaro da za su bi layi-layo don hukunta masu kunnen ƙashi.