Ganduje ya Rantsar da Kwamitin Shirya Makon Tunawa da Tsofaffin Sojoji ta Bana

Date:

Daga Zara Jamil Isa
 Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da kwamitin Tsare-tsare na Ranar Tunawa da Sojoji ta 2022.
 Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, wanda ya kaddamar da kwamitin, ya bukaci mambobin Kwamitin da su fito da wani tsare wanda zai zarce na bara.
 Cikin wata sanarwa da Daraktan aiyuka na Musamman Kuma jami’in yada labaran Ma’aikatar yada labaran Sani  Abba Yola be ta aikowa Kadaura24 Sanarwa wadda ya Sanyawa Hannu.
Sanarwar tace Babban Sakataren ma’aikatar, Alhaji Usman Bala Muhammad ne ya wakilce Kwamishinan Ma’aikatar Com. Muhd Garba, Inda ya ce ranar tunawa da tsafaffin sojoji da kuma tattara kudin da za’a taimakawa iyalansu, taron ne na shekara-shekara da ake shiryawa musamman don karrama Yan mazan jiyan wadanda suka bada Gudunmawa wajen Kare martabar Najeriya.
 Babban Sakatare ya bayyana cewa, don jin dadin sadaukarwar da jaruman da suka mutu suka Gudanar za a samar da kudaden ne don tallafa wa iyalansu da ke matukar bukatar kulawa da ta Musamman.
 Usman Bala ya ce wannan biki ne na tsawon mako guda kuma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne Zai jagoranci Sanya fure domin girmamawa ga tsaffin Sojojin  ya yin Babban taron.
 Ya ce aiyukan kwamitin sun hadar da tsara makon na tunawa da rundunar soji ta shekarar 2022 da kuma tabbatar da cewa an samar da duk wasu shirye-shiryen da suka dace domin samun nasarar gudanar da bikin tunawa da sojojin na shekarar 2022 da dai sauransu.
Sanarwar tace Kwamitin yana karkashin kwamishinan yada labarai, sai Babban sakataren yada labarai, a matsayin mataimakin shugaba;  yayin da darakta, Harkokin Cikin Gida na ma’aikatar zai zama Sakataren kwamitin.
 Wakilan kwamitin sun fito ne daga Rundunar Sojojin Najeriya, Navy, Air Force, DSS, Civil Defence Corps, Special, Services, Nigerian Legion, Protocol Directorate, Fire Service da kuma ma’aikatar yada labarai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu matasan Kano biyu a Benue

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi...

Rashin Jami’ar Mallakin jihar a shiyyar Kano ta Arewa na kokarin bayar da yankin baya – Alh. Mustapha Ahmad Gwadabe

Daga Shehu Hussaini Ahmad Getso An bukaci Gwamnatin jihar Kano...

Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Almuharram a Nigeria

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji...

Yan uwan wata mata sun zargi Asibitin Malam Aminu Kano da sakaci wajen mutuwar yar uwarsu

Daga Sadiya Muhammad Sabo   Yan uwan wata mata da ta...