Daga Zara Jamil Isa
Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da kwamitin Tsare-tsare na Ranar Tunawa da Sojoji ta 2022.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, wanda ya kaddamar da kwamitin, ya bukaci mambobin Kwamitin da su fito da wani tsare wanda zai zarce na bara.
Cikin wata sanarwa da Daraktan aiyuka na Musamman Kuma jami’in yada labaran Ma’aikatar yada labaran Sani Abba Yola be ta aikowa Kadaura24 Sanarwa wadda ya Sanyawa Hannu.
Sanarwar tace Babban Sakataren ma’aikatar, Alhaji Usman Bala Muhammad ne ya wakilce Kwamishinan Ma’aikatar Com. Muhd Garba, Inda ya ce ranar tunawa da tsafaffin sojoji da kuma tattara kudin da za’a taimakawa iyalansu, taron ne na shekara-shekara da ake shiryawa musamman don karrama Yan mazan jiyan wadanda suka bada Gudunmawa wajen Kare martabar Najeriya.
Babban Sakatare ya bayyana cewa, don jin dadin sadaukarwar da jaruman da suka mutu suka Gudanar za a samar da kudaden ne don tallafa wa iyalansu da ke matukar bukatar kulawa da ta Musamman.
Usman Bala ya ce wannan biki ne na tsawon mako guda kuma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne Zai jagoranci Sanya fure domin girmamawa ga tsaffin Sojojin ya yin Babban taron.
Ya ce aiyukan kwamitin sun hadar da tsara makon na tunawa da rundunar soji ta shekarar 2022 da kuma tabbatar da cewa an samar da duk wasu shirye-shiryen da suka dace domin samun nasarar gudanar da bikin tunawa da sojojin na shekarar 2022 da dai sauransu.
Sanarwar tace Kwamitin yana karkashin kwamishinan yada labarai, sai Babban sakataren yada labarai, a matsayin mataimakin shugaba; yayin da darakta, Harkokin Cikin Gida na ma’aikatar zai zama Sakataren kwamitin.
Wakilan kwamitin sun fito ne daga Rundunar Sojojin Najeriya, Navy, Air Force, DSS, Civil Defence Corps, Special, Services, Nigerian Legion, Protocol Directorate, Fire Service da kuma ma’aikatar yada labarai.