Daraktan Fim din Makaranta Wanda ake koyar da Jima’i Yace Ba Don Mutanen Kano Suka Shirya Fim din Su Ba

Date:

Daraktan fim din nan da ake ta yin tallansa mai suna ‘Makaranta’ ya ce bai damu da barazanar da hukumar tace fina-finan Jihar Kano ta yi na kama shi ba.

Hukumar tana neman Aminu Umar Mukhtar ne ruwa a jallo, inda take zargin sa da lalata tarbiyya da kuma rashin bin ka’ida yayin fitar da tallan fim din.

Fim din ‘Makaranta’ ya nuna abubuwa da dama da mutane da dama suke ganin ba su dace a yi fim a kansu ba, wadanda suka hada da madigo da batsa da makamatansu.

Hakan ne ya sa shugaban hukumar tace fina-finan ta Kano, Isma’ila Na’abba Afakallah, ya shaida wa BBC cewa sun aika wa daraktan takardar gayyata a watan jiya domin ya je gabansu ya yi musu bayani na dalilan da suka sa ya soma tallan fim din ba tare da samun izininsu ba.

A cewarsa, Aminu Umar Mukhtar ya shaida musu cewa zai zo gabansu idan aka shiga sabuwar shekara amma bai je ba, lamarin da ya sa suka fara nemansa ruwa a jallo.

Afakallah ya kara da cewa za su tuhumi daraktan fim din bisa laifukan da suke ganin ya aikata.

Ba don mutanen Kano na yi fim din ba

Sai dai a tattaunawarsa da BBC, Aminu ya kare kansa bisa fitar da tallan fim din, yana mai cewa bai damu da neman da hukumar tace fina-finan Kano ke yi masa ba.

“Na samu labarin cewa hukumar tace fina-finan Kano tana nema na. Ban yi ko gezau ba domin kuwa ban aikata wani laifi ba,” in ji shi.

“Fim din da na yi ba a kan mutanen Kano ko Hausawa na yi ba, na yi amfani da harsuna 17 a cikinsa. Kuma ba a Kano aka dauki fim din ba, don haka ban san dalilin da ya sa ya zama abin ce-ce-ku-ce ba.

“Fim dina ba kawai yana magana ba ne game da ilimin jima’i ba, yana kuma nuna illolin kaciyar mata da wayar da kai kan abubuwan da ke faruwa a tsakanin Hausawa da ma wasu al’ummomi.”

BBC Hausa ta rawaito Daraktan fim din na ‘Makaranta’ ya musanta cewa wasu ne suke daukar nauyin sa domin ya bata tarbiyyar mutane.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...