An yi Kira ga al’ummar Musulmi a Jihar Kano da su Maida hankali wajen cigaba da yiwa Kasar nan addu’o’in Samun hadin Kai da dawwamamen Zaman Lafiya.
Wani Malamin addinin Musulci a nan kano, Malam Nasiru Liman Gwammaja ne ya bayyana hakan yayin addu’ar sadakar 7 ta mahaifiyar Yahya Adamu Garin-Ali, Wato Hajiya Fatima Adamu.
Malam Nasiru Liman Gwammaja yace Kiran ya Zama wajibi Idan akai la’akari da halin Rashin tsaro da ake Cikin da ake Ciki a Kasar nan da Kuma tsadar Kayan masarufi, sannan yayi addu’ar Allah ya gafartawa Hajiya Fatima yasa aljannar fiddausi ta zamo makomarta.
A nasa Jawabin Guda Cikin Masu neman tsayawa takarar Gwamnan Jihar Kano a jam’iyyar APC Alhaji Abdulkarim Abdussalam A A Zaura ya yi Fatan Marigayiyar zata Sami rahamar Ubangiji, Sannan yayi fatan Malamai zasu cigaba da yiwa Kasar nan addu’o’in Samun Zaman Lafiya da Kawo Karshen Matsalolin tsaro da suka addabi Nigeria.
A Jawabinsa Guda Cikin’ya’yan Marigayiyar Kuma Babban Darkatan A Hukumar Samar da hanyoyi a yankunan karkara ta jihar Kano Dr. Yahya Adamu Garin-Ali ya godewa al’umma Waɗanda suka halarci addu’ar da ma Waɗanda suka je don yi musu ta’aziyya Rasuwar mahaifiyar tasu tare da fatan Allah ya sakawa kowa da alkhairi.