Daga Abubakar Sa’eed Sulaiman
Shugaban Jarumai masana’antar Kanywood Alhassan Kwalle ya barranta masana’antar su ta Kanywood da Wani Shirin fim da Yanzu haka ake tallansa a YouTube.
Alhassan Kwalle ya bayyana hakan ne yayin wata Ganawa da yayi da Wakilinn Kadaura24 a Ofishin sa.
Alhassan Kwalle yace Shirin da ake tallafan ya sabawa koyarwa ta addinin Musulci da al’adun Hausawa da kuma dokokin masana’antar don haka suke barranta kansu da fim din.
Shugaban Jaruman ya Kuma ce zasu tabbatar da Cewa zasu dauki matakan da suka dace na shari’a akan Wanda ya Shirya fim din ,duk da mashiryin Shirin ba don masana’antar ba ne.
“Mun yi waya da mashiryin Shirin domin in Sanar da Shiri cewa abun da sukai ba dai-dai bane, Amma tun a tashin fari yace shi fa ba dan Kanywood bane, ya Shirya Shirin ne a karan Kansa”. Inji Alhassan Kwalle
Kwalle ya ce yana da yakinin Hukumar tace Fina-finan ta Jihar Kano bazata bar abun sakakaba, yasan zata dauki Matakin daya dace domin hana Fitar da fim din don gudun lalata tarbiyyar al’umma.
A Jawabinsa Shugaban Hukumar tace Fina-finan Hausa ta Jihar Kano Isma’ila Na-Abba afakallah yace zasu lamunci irin badala a Cikin Fina-finai ba , Inda ya bayar da tabbacin Hukumar zata lalubo Mashiryin Shirin domin gurfanar da shi a gaban shari’a.
Yayin Zantawarsa da Manema labarai Afakallah yace Aikin Hukumar ne ta hana yin fim din da ya sabawa addinin Musulci da al’adun Malam Bahaushe a don tabbatar da sauke nauyin da Gwamnati ta dora Mata.