Ba da Wanda Muke Maganar Zan Koma APC – Sanata Kwankwaso

Date:

Daga Nura Abubakar Darma

Tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa bashi da Wani Shiri na barin jam’iyyar sa ta PDP Zuwa Jam’iyyar APC Mai Mulkin Nigeria.
Sanata Kwankwaso ya bayyana hakan ne Cikin Wata Hira da yayi da Gidan Radio na DW dake Kasar Jamus.
Gidan Radio ya rawaito Sanata Kwankwaso ya na cewa a Yanzu dai bashi da Wata niyya ta barin jam’iyyar PDP Zuwa APC Kamar yadda ake ta jita-jitar zai bar jam’iyyar Saboda Rashin Yi da shi da ba a yi a jam’iyyar.
Maganar sauya Sheka Babu ita a yanzu din nan, bana Magana da Wasu Mutane Kan cewar Zan Koma APC” inji Kwankwaso
“Amsar da tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayar dangane da jita-jitar da ake yadawa kan cewa zai sauya sheka daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC”. Gidan Radio ya rawaito
Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito Cewa an Fara tunani Kwankwaso da Ganduje zasu yi Sulhu ne tun bayan da Gwamna Ganduje ya Kaiwa Sanata Kwankwason Ziyarar ta’aziyyar kaninsa da ya rasu a kwanakin baya.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...