Daga Ali kakaki
Shugaba kuma wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha American University a Nijer da Nijeriya, sannan kuma shugaban kungiyar Jami’o’i masu zaman kansu ta Afrika, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya bayyana cewa hassada da bakin ciki da ake yi a nahiyar Afrika ne ya hana nahiyar ci gaba.
Farfesan ya bayyana hakan ne a taron taya shi murnar cika shekara 44 Wanda ya gudana a ranar 1 ga watan Janairun 2022 a Otel din Bristol dake birnin Kano.
Shugaban jamiar ta (FBIU) kaduna farfesa Gwarzo ya bayyana cewa; “Abin da na fada da yake tada hankali a Afrika shi ne hassada. Yana da kyau a Afrika mu dunga ganewa cewa hassadar da muke yi wa juna ita ce take mayar da Afrika baya.
“Za ka ga mutum ya fara tasowa, yana kokari, sai ka ga makiya suna neman kawo shi kasa. To idan ka ga mutum yana kokari abin da ya dace ka yi masa shi ne ka taimake shi. Saboda haka bai dace a ce don ka ga wani zai yi Jami’a ko yana cigaba ka dunga neman hanyar da za ka dake shi ko za ka hana shi ci gaba ba”, ya jaddada.
Har wa yau Farfesa Gwarzo ya nusasshe da jama’a da cewa; “Yana da kyau jama’a mu tashi tsaye mu taimaki juna. Afrika tana cikin bala’i. Kullum sai ku rika zuwa Turai kuna kallon Turai, to abin da ya daga Turai babu hassada. Yanzu ga irin su Farfesa Saluhu nan, ba ga shi Faransa ta rike su ba. Idan suka ga kana da kyau rike ka za su yi! Saboda me? Saboda ka baiwa kasar su gudunmawar ta ci gaba”.
Duk a cikin jawabinsa a taron, Farfesa Gwarzo ya yi nuni da cewa akwai bukatar al’umma su kaunaci junansu tare da taimakon junansu, inda yake cewa; “yana da kyau jama’armu mu rika son juna, mu rika taimakon juna, ba wai ake murnar Gwarzo-Gwarzo ba, ni ai a yi ta taya ni murna ba shi ne muhimmanci a waje na ba, nima naga na zo na taya wasu murna shi ne muhimmanci na”.
Ya ci gaba da cewa; “Idan ni kadai ake taya murna mene ne amfanin taya ni murna ni kadai? Kullum a zo ana ‘Barka da karin shekara. Kai Gwarzo ne, da sauran su’, wannan ba komai bane, Gwarzo ya riga ya yi nasara, sauran nake so su ma su yi nasara, mu zo mu taya su murna. Nima na zo na ce wane abin koyina ne, ya burge ni. Ba wai ni kullum a rika kirana abin koyi ba, wannan ba shi ne manufata ba, ni manufa ta a samu Adamu Abubakar Gwarzo a Kano akalla mutum 500. Jama’armu ya dace mu zauna mu dunga bai wa juna shawara, mu dunga ba juna shawara, duk inda hassada take mu kore ta. Da kun ga mutum ya kawo ci gaba, ku mara mai baya saboda a karshe ci gaban ba na shi bane na al’umma ne. Ci gaba na al’umma ne. Ci gaban ba na shi bane na al’umma ne”, ya jaddada.
Ya kara da cewa; “Yanzu bari na ba ku misali, yanzu ni a kudina nawa zan kashe? Gaba daya nawa zan kashe? To amma idan na samu kudin ai al’umma zan ba kudin, idan ka da ga al’umma da yawa suka samu arziki, to ina tabbatar muku cewa garinku zai ci gaba”, ya lurantar.